Wadanda Buhari ya nada sun yi kasa a gwiwa wajen kawo tsaro – Zanna Boguma

Wadanda Buhari ya nada sun yi kasa a gwiwa wajen kawo tsaro – Zanna Boguma

- Wani Basarake a kasar Borno, Zanna Boguma ya koka game da matsalar tsaro

- Zanna Boguma ya ce Gwamnatin Buhari ba ta yi wa Yankin Arewa kokari ba

- Boguma ya ke cewa manyan Arewa sun takawa gwamnatin Buhari rawar gani

Wani babba daga cikin manyan kasar Borno, Zanna Boguma ya ce rikicin Boko Haram da kashe-kashen da ake yi ya nuna har yanzu akwai sauran rina a kaba.

Alhaji Zanna Boguma ya yi kuka da garkuwa da mutane da ta’adin da ake gani a cikin kasar nan, ya ce hakan ya nuna gwamnatin Muhammadu Buhari ta gaza.

Dattijon ya ke cewa gwamnatin APC mai ci, ba ta iya shawo karshen matsalar tsaro ba. Boguma ya bayyana wannan ne a lokacin da ya yi wata hira da Arewa Agenda.

Wannan Bawan Allah wanda ya ke rike da sarautar Zanna Boguma na kasar Borno, ya na zargin gwamnatin Buhari da gaza yin abin da ya dace wajen taimakon Arewa.

A cewar jigon na kungiyar dattawan Arewa ta NEF, yankin Arewacin kasar sun bada gudumuwa sosai a zaben da ya ba Muhammadu Buhari da jam’iyyarsa ta APC nasara.

KU KARANTA: Rikicin Kaduna: Zamani Lekwot ya yi magana game da kiran a hukunta shi

Wadanda Buhari ya nada sun yi kasa a gwiwa wajen kawo tsaro – Zanna Boguma
Shugaban kasa Buhari da wasu manyan Borno
Asali: Twitter

Ya ce miyagun ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda irinsu Boko Haram su na kashe mutanen Arewa har gobe ba tare da alamun za a kawo karshen wannan mummunan lamari ba.

“Idan ana maganar Najeriya, shugaba (Buhari) ne kurum wanda ya ba mutanenmu mukamai, amma ba su yi komai na cigaba ba.” Zanna ya fadawa Arewa Agenda.

Zanna Boguma ya ce kungiyarsu ta NEF ta yi kokari wajen ganin Buhari ya karbi mulki, daga cikin gudumuwar da su ka bada har da shawo kan Amurka ta mara masa baya.

Wannan mutumi mai rike da sarautar gargajiya ya ke cewa ya na cikin wakilan da NEF ta tura zuwa birnin Washington, domin a karkato da ra’ayin masu ta-cewa a ketare.

Shekara biyar kenan a mulki, amma APC ba ta kawo karshen abin da ta zargi gwamnatin baya da yi ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel