Da duminsa: Shugaban jam'iyyar APC na jihar Akwa Ibom ya rasu

Da duminsa: Shugaban jam'iyyar APC na jihar Akwa Ibom ya rasu

- Shugaban jam'iyyar APC na jihar Akwa Ibom, Ini Okopido ya mutu

- Ya rasu ne a ranar Laraba sakamkon rashin lafiya a asibitin Ibom Multi specialty Hospital da ke Uyo

- Wani jigon jam'iyyar a jihar ne ya tabbatar da hakan a sa'o'in farko na yau Laraba

- Ya bayyana cewar jam’iyyar mai mulki a kasar ta shiga alhini na wannan rashi da ta yi

Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na jihar Akwa Ibom, Ini Okopido ya rasu.

Wani jigo a jam'iyyar a jihar ne ya tabbatar da hakan a sa'o'in farko na ranar Laraba. Lamarin ya auku ne a asibitin Ibom Multi specialty Hospital da ke Uyo.

KU KARANTA KUMA: A binciki sarakunan gargajiya a yankunan da rashin tsaro ya tsananta - Sanata Gobir

Da duminsa: Shugaban jam'iyyar APC na jihar Akwa Ibom ya rasu
Da duminsa: Shugaban jam'iyyar APC na jihar Akwa Ibom ya rasu Hoto: The Nation
Asali: UGC

Kamar yadda majiyar tace, Okopido ya rasu ne sakamakon gazawar wasu sassa na jikinsa.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Sojoji da ‘yan sanda sun kama masu zanga-zanga a Abuja

"Tabbas shugabanmu ya rasu. A takaice, dukkan jam'iyyar APC ta jihar tana juyayi. Babban rashi ne ga jam'iyyar a fadin kasar nan.

"Muna ta'aziyyar ga matarsa da 'ya'yansa a kan wannan babban rashin," yace a tattaunawar waya.

A wani labarin kuma, mun ji cewa Kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC) ta sanar da rasuwar tsohon manajan daraktanta, Dr Joseph Thlama Dawha.

Dr. Dawha ya rasu ne bayan gajeriyar rashin lafiya, manajan bangaren hulda da jama'a, Dr. Jennie Obateru ya sanar a wata takarda a ranar Litinin da dare.

Manajan daraktan kamfanin, Malam Mele Kyari, ya nuna matukar damuwarsa a kan mutuwar farat daya da Dr. Dawha yayi, wanda shine manajan darakta na 16 na kamfanin.

Malam Kyari ya ce daukacin NNPC ta na jimami tare da ta'aziyyar mutuwar tsohon GMD Dawha.

Ya tabbatar da cewa ya taimaka wurin shugabanci tare da bada gudumawa a bangarorin ci gaba da kamfanin.

Ya bayyana mutuwar Dr. Dawha a matsayin babban rashi ga NNPC tare da Najeriya baki daya.

Dawha ne GMD na kamfanin tsakanin watan Augustan 2014 zuwa watan Augustan 2015.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel