Ana Rikicin ADC, Nafiu Bala Ya Fito da Maganganu kan Tinubu da Atiku
- Nafiu Bala ya bayyana cewa shi ne sahihin shugaban tsagin jam'iyyar ADC bayan hukuncin da kotu ta yi a kan rikicin cikin gida da suke yi
- A bayanan da ya yi, Nafiu Bala ya yi bayani kan yadda ya samu jami'an tsaron da suke kare shi daga barazanar da ya ke fuskanta
- Hakan na zuwa ne yayin da bangaren Atiku Abubakar ke nuna cewa su ne sahihan masu rike da jam'iyyar duk da ikirarin Nafiu Bala
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Yayin da ake shirin 2027, Nafiu Bala ya sake maganganu game da rikicin cikin gida da suke fuskanta a jam'iyyar ADC a Najeriya.
Nafiu Bala ya bayyana cewa shi ne sahihin shugaban ADC bayan kotu ya rusa shugabancin David Mark na bangaren Atiku Abubakar.

Source: Facebook
A wata hira da BBC Hausa ta yi da Nafiu Bala da ta wallafa a X, ya bayyana cewa yanayin dimokuradiyya na tafiya daidai a Najeriya.
Nafiu Bala ya kare Tinubu
Game da yadda yan adawa ke korafi a karkashin mulkin shugaba Bola Ahmed Tinubu, Nafiu Bala ya bayyana cewa shi bai ga wani abin korafi ba.
A bayanan da ya yi, ya ce komai na tafiya daidai saboda a ganin shi ana ba kowane dan adawa damar gudanar da harkokin shi.
Ya ce:
'A ganina dimokuradiyya na tafiya daidai."
Game da sukar shugaba Bola Tinubu, Nafiu Bala ya bayyana cewa:
"Ba zai yi wa yau saboda mu 'yan adawa ne mu rika daukar munanan kalamai muna jifar juna da su. Ban yarda da wannan ba, kuma ba zan yi ba."
A bayanan da ya yi, Nafu Bala ya kara da cewa ana ba jam'iyyun adawa dama su gudanar da harkokinsu ba tare da wata matala ba.
Ya kara da cewa hukuncin da kotu ta yi ya nuna gaskiya kuma suna mika godiya ga Allah a kan abin da aka tabbatar bayan shari'ar da aka yi.
Ya ce sun samu takardar hokuncin da aka yi kuma za su jira matakin da za a dauka domin cire sunan David Mark a sanya na shi.
An ba Nafiu Bala tsaro
Nafiu Bala ya tabbatar da cewa hukumomin Najeriya sun ba shi jami'an tsaro na musamman domin ba shi cikakkiyar kariya.
Ya ce doka ta tanadi cewa za a ba shi tsaro kamar yadda aka ba shugabannin jam'iyyun LP, APC, PDP da sauransu a Najeriya.
Hon. Nafiu Bala ya bayyana cewa kamar yadda Atiku zai nemi jami'an tsaro haka shi ma yake da hakkin neman jami'an a kundin tsarin mulki.

Source: Twitter
Korafin 'yan ADC a Arewa
A wani labarin, kun ji cewa shugabannin ADC na Arewacin Najeriya sun yi Allah wadai da matakin da kotu ta dauka na rusa shugabancin David Mark.
Sun bayyana cewa akwai siyasa a lamarin, kuma za su yi duk abin da ya dace domin ganin an dawo da David Mark shugabancin ADC.
Hukuncin da kotu ta yanke ya nuna cewa dukkan matakan da David Mark ya dauka sun rushe ciki har da takarar Atiku Abubakar.
Asali: Legit.ng

