Aiki Ya Dake Baya: Kotu Ta Rushe Zaɓen Fitar da Gwani Dan Takarar ADC a Kaduna

Aiki Ya Dake Baya: Kotu Ta Rushe Zaɓen Fitar da Gwani Dan Takarar ADC a Kaduna

  • Kotun Tarayya da ke Kaduna ta soke zaben fitar da gwani na jam'iyyar ADC da aka gudanar domin zaben dan takarar kujerar Majalisar Wakilai ta Ikara/Kubau
  • Alkalin kotun ya ce an gudanar da zaben ne ba tare da bin ka'idojin doka da tsarin jam'iyyar ba, lamarin da ya sa sakamakon ya zama mara inganci
  • Hukuncin ya biyo bayan karar da Ibrahim Dallami Kubau ya shigar kan jam'iyyar ADC da wasu mutum biyu gabanin babban zaben 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna – Kotun Tarayya da ke Kaduna ta soke zaben fitar da gwani na jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) da aka gudanar domin zaben dan takarar kujerar Majalisar Wakilai ta tarayya mai wakiltar mazabar Ikara/Kubau.

Kotun ta yanke hukuncin ne a ranar Alhamis, 12 ga watan Nuwamba, 2026, bayan sauraron karar da Ibrahim Dallami Kubau ya shigar kan jam'iyyar ADC da wasu mutum biyu.

Kara karanta wannan

Jiragen sama sun yi ruwan wuta kan ƴan ta'adda, an kashe miyagu 40

Legit Hausa ta samu cewa zaben fitar da gwani da kotun ta soke shi ne wanda ya samar da Mustapha Aliyu Abdullahi a matsayin dan takarar jam'iyyar mai wakiltar mazabar Ikara/Kubau a zaben 2027.

Kotun ta gano kura-kurai a zaben ADC

A hukuncin da ta yanke, kotun ta bayyana cewa tsarin gudanar da zaben fitar da gwani bai bi ka'idojin doka da kuma dokokin cikin gida na jam'iyyar ADC ba.

Alkalin kotun ya ce gazawar bin wadannan ka'idoji ta sa zaben ya rasa ingancin da ake bukata domin amincewa da sakamakonsa.

Bayan hukuncin, nadin Mustapha Aliyu Abdullahi a matsayin dan takarar jam'iyyar ADC a mazabar ya rasa ingancin da yake da shi a karkashin wannan zabe.

Abin da hukuncin ke nufi ga ADC

Hukuncin na nufin cewa jam'iyyar ADC za ta sake duba batun wanda zai wakilce ta a kujerar Majalisar Wakilai ta Ikara/Kubau a babban zaben 2027.

Dokokin zabe a Najeriya sun tanadi cewa dole ne jam'iyyun siyasa su gudanar da zabukan fitar da gwani bisa tanade-tanaden dokar zabe da kuma ka'idojin da suka shimfida wa kansu.

Duk wani sabawa wadannan ka'idoji na iya janyo kalubalantar zaben a kotu tare da soke sakamakonsa.

Kara karanta wannan

Yadda hukuncin kotu ya sake kara damuwar da Atiku da jam'iyyar ADC ke ciki

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, jam'iyyar ADC da sauran wadanda aka shigar da karar a kansu ba su fitar da sanarwar mayar da martani kan hukuncin ba.

Wata kotu ta kori dan takarar NDC a Edo

A wani labarin makamancin haka, Legit.ng ta ruwaito cewa wata Kotun Tarayya da ke Benin City ta kori Uyi Omosigho daga matsayin dan takarar jam'iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) mai neman kujerar Majalisar Wakilai ta mazabar Oredo.

Kotun ta kuma ayyana Omo-Osagie Efosa, wanda aka fi sani da Mighty Man, a matsayin halastaccen dan takarar jam'iyyar a mazabar.

Alkalin kotun, Farfesa Chuka Obizor, ya kuma nuna rashin jin dadinsa kan abin da ya bayyana a matsayin matakan da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ke dauka wadanda ke kawo cikas ga shari'o'in da suka shafi harkokin zabe kafin gudanar da zabe.

Karin bayani na tafe ....

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.