Yadda ‘Yan Sanda Suka Garkame Farfesa Zulum saboda Ya Nemi Tsayawa Takara a Borno
- Gwamnan Borno ya ce yadda ’yan sanda sun taɓa tsare shi don kawai ya nuna sha’awar neman kujerar siyasa
- A shekarun baya, Babagana Umara Zulum ya yi harin tsaya takarar shugaban ƙaramar hukumar Mafa a Borno
- Sai aka zarge shi da shiga ƙungiyar NADECO da tunzura jama’a, hakan ya sa jami’an ‘yan sanda suka yi ram da shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Borno - Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana yadda ’yan sanda suka taɓa tsare shi saboda burinsa na siyasa.
Farfesan ya ce a dalilin ya bayyana aniyarsa ta neman kujerar shugabancin ƙaramar hukumar Mafa da ke jihar Borno, aka cafke shi.
'Yan sanda sun taba kama Babagana Zulum
Daily Trust ta ce Babagana Zulum ya bada labarin ne ranar Laraba wajen ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar APC a jihar Borno.
Zulum ya ce abin da ya faru a Mafa shi ne karo na farko kuma na ƙarshe da ya taɓa nuna sha’awarsa ta tsayawa takarar zaɓe a rayuwarsa.
Da yake ba da labarin abin da ya faru, gwamnan ya fada wa 'yan siyasa yadda aka yi masa sharri.
"Na kasance a Mafa ina ɗebo ruwa daga rijiya, hannuwana sun yi rauni har suna zubar da jini. A lokacin ne na bayyana sha’awata ta neman kujerar, tare da addu’a ga Allah Ya ba ni damar samar da rijiyoyin burtsatse a Mafa.
"Amma wasu mutane suka kai rahoton cewa na shiga ƙungiyar NADECO ko wani abu makamancin haka, cewa suna ƙoƙarin tunzura jama’a a kan jami’an ƙaramar hukumar. Saboda haka aka tsare ni."
- Babagana Zulum
An kafa hukumar NADECO ne a lokacin marigayi Janar Sani Abacha domin yaki da mulkin soji.
Zulum ya yi maganar wahala siyasa da mulki
Gwamnan na jihar Borno ya bayyana cewa tsare mutane a wasu lokuta na iya kasancewa cikin abubuwan da ke faruwa a harkar siyasa a Najeriya.
Ya ƙara da cewa ba zai yi mamaki ba idan ’yan sanda suka kama wani saboda sha’anin siyasa.

Kara karanta wannan
Abdulaziz Yari ya fada wa Tinubu ya je ya yi barci, APC ta ci zabe ta gama a Arewa
Haka kuma, Zulum ya yi magana kan nauyin shugabanci, inda ya ce tafiyar da gwamnati na buƙatar sadaukarwa, haƙuri da kuma jajircewa.
Sannan ya bayyana cewa a kullum ba ya tashi daga ofis sai tsakanin ƙarfe 11:30 na dare zuwa 1:30 na dare saboda yawan ayyukan da ke gabansa.
Akwai hannun Zulum a kama 'yan TinubuMustGo?
Gwamnan ya kuma yi tsokaci kan sukar da ake yi masa, ciki har da zargin da ya shafi kama masu zanga-zangar "Tinubu Must Go" a Borno.
Jaridar Yerwa Express ta ce gwamna Zulum ya musanta sanin abin da ya faru tun kafin lokacin, yana mai cewa bai da labari said aga baya.
Duk da haka Mai girma gwamnan ya dauki alhaki saboda shi jama'an Borno su ka ba amanar kuri'unsu.
Kira ga 'yan kwamitin yakin neman zaben APC
Zulum Ya kuma yi kira na musamman ga ’yan majalisar wakilai da na majalisar dokokin jihar Borno da suka rasa takara a APC da su yi haƙuri.
Ya buƙaci mambobin kwamitin yaƙin zaɓen da aka ƙaddamar, wanda shi ne shugabansa, da kada su dogara da nasarorin da suka samu a baya.
Ya ce dole su koma mazabu da rumfunan zaɓensu don neman goyon bayan jama’a su zabi Bola Tinubu, Mustapha Gubio da sauran ‘yan APC.
Asali: Legit.ng
