Mutuwa Ta Girgiza Fannin Ilimi a Najeriya, Tsohon Shugaban OAU Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- Farfesa Wale Omole, tsohon shugaban jami'ar Obafemi Awolowo, ya rasu ranar Larabada ta gabata yana da shekaru 84 a duniya
- Marigayin ya rike mukamin shugaban jami'ar OAU (VC) daga 1991 zuwa 1999, kuma shi ne tsohon dalibi na farko da ya kai wannan matsayi
- Omole ya kafa gidauniya domin inganta ilimi, ci gaban al'umma da kare al'adun Yarbawa kafin rasuwarsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Osun, Nigeria - Tsohon shugaban jami'ar Obafemi Awolowo (OAU) da ke jihar Osun, Farfesa Wale Omole, ya rasu yana da shekaru 84.
Marigayin ya rasu ne a ranar Laraba, 11 ga Nuwamba, 2026, a gidansa, kamar yadda shugaban kungiyar Ijesa Society, Lateef Bakare, ya sanar a cikin wata sanarwa da ya fitar jiya Laraba.

Source: Facebook
Farfesa Wale Omole ya rasu
Bakare ya bayyana cewa Omole babban jigo ne a kungiyar, kuma ya kasance daya daga cikin fitattun 'ya'yan kabilar Ijesa, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
A cikin sanarwar, ya ce:
"Cikin godiya ga Allah bisa rayuwar da ya yi mai amfani, kuma a madadin iyalan Omole da gidan sarautar Biladu na kasar Ijesa, ina mai bakin cikin sanar da rasuwar mahaifinmu, dan'uwanmu, abokinmu kuma dan kasa, Farfesa Adebowale Omole, MON.
"Farfesa Wale Omole ya rasu cikin kwanciyar hankali a gidansa da sanyin safiyar Laraba, 11 ga Nuwamba, 2026. Ya yi bikin cika shekaru 84 da haihuwa a ranar 13 ga Agusta, 2026.
"Ya kasance mai kishin al'ummar Ijesa, kuma jajirtaccen mamba a kungiyar mu har zuwa wannan lokaci. Za a sanar da shirye-shiryen jana'izarsa bayan iyalansa sun kammala tsara komai."
Bakare ya kuma mika sakon ta'aziyya a madadin Mai Martaba Owa na Ijesaland, Clement Adesuyi Haastrup, Ajimoko III, inda ya bayyana marigayin a matsayin daya daga cikin manyan mutane da kasar Ijesa ta taba samu.
Ya bukaci mambobin kungiyar su sanya iyalan marigayin cikin addu'o'insu a wannan lokaci mai muhimmanci, tare da fatan Allah ya jikansa.
Tarihin rayuwar Farfesa Omole
Marigayin masanin kimiyyar dabbobi ne, jami'in gudanar da harkokin jami'a, kuma mai fafutukar farfado da al'adun Yarbawa.
Shi ne tsohon dalibi na farko a jami'ar Ife, wadda a yanzu ake kira Obafemi Awolowo University, da ya zama shugaban jami'ar. Ya rike mukamin daga shekarar 1991 zuwa 1999.
Sai dai an cire shi daga mukamin ba tare da bata lokaci ba bayan zanga-zangar dalibai, wadanda suka zarge shi da alhakin wani hari da kungiyar asiri ta kai kan dalibai wanda ya yi sanadin mutuwar mutum biyar.
Gudummawarsa ga ilimi da al'adu
Omole ya kuma taba zama shugaban editocin jaridar The Guardian. Haka kuma, ya kafa gidauniya mai mayar da hankali kan ilimi, ci gaban al'umma da kyawawan dabi'un Yarbawa.

Source: Facebook
A watan Agustan 2024, ya kaddamar da gidauniyar Wale Omole Foundation for Virtues and Ethics in Yoruba Culture a Legas.
Ya gina manufar gidauniyar ne bisa koyarwar Yarbawa ta 'Omolúàbí', wadda ke karfafa mutum ya kasance mai kyawawan dabi'u da halin kirki a rayuwar jama'a da ta kashin kai.
Kun ji cewa
Asali: Legit.ng

