Kamfanin Shoprite ya bada sanarwar zai daina kasuwanci a Najeriya

Kamfanin Shoprite ya bada sanarwar zai daina kasuwanci a Najeriya

- Shoprite za su yi gwanjon kaya, su na shirin barin kasuwanci a Najeriya

- Kamfanin kasar Afrika ta Kudun ya shafe shekaru akalla 15 a kasar nan

- Bisa dukkan alamu dai kamfanin ba ya cin ribar kasuwancin da ya ke yi

Shararren kamfanin nan na Shoprite masu katafaren shaguna a kasashen Afrika har da Najeriya, sun bada sanarwar cewa za su fice daga kasar nan.

Rahotanni sun ce bayan shekaru 15 su na kasuwanci a Najeriya, Shoprite za su bar Najeriya. Kamfanin zai yi gwanjon kayan da ya rage masa ya bar kasar.

Shoprite ya bada wannan sanarwa ne a ranar Litinin, 2 ga watan Agusta, 2020. Hakan na zuwa ne bayan kamfanin ya fitar da bayanin yadda kasuwancinsa ya ke tafiya.

Rahoton kasuwancin Shoprite da ya fito karshen watan Yuni ya nuna cewa kamfanin kasar wajen ya na fuskantar kalubale wajen aiki a kasar Najeriya.

Kafin Shoprite, kamfanin Mr. Price da Woolworths sun bar Najeriya a baya. Duk wadannan kamfanonin kasar Afrika ta kudu ne da ake ji da su a Nahiyar nan.

KU KARANTA: Coronavirus ta saki Jarumin Indiya Amitabh Bachchan

Kamfanin Shoprite ya bada sanarwar zai daina kasuwanci a Najeriya
Wani shagon Shoprite
Asali: Getty Images

A jawabin da kamfanin ya fitar, ya ce sakamakon ribar kasuwancinsu ya nuna zamansu ya kare a Najeriya, hakan na nufin asarar da Shoprite ya ke yi, ya yi kamari.

Cinikin da kamfanin ya ke yi ya yi kasa da 1.4% daga shekarar 2018 zuwa yanzu. Karancin cinikin kamfanin ya karu sosai a lokacin da aka hana fita saboda COVID-19.

A dalilin takunkumin COVID-19, sai da cinikin Shoprite ya yi kasa da 7.4%, ko da dai masu yi wa kamfanin ciniki su kan cika kwandonsu a wannan lokaci.

Wannan lamari zai iya sa dinbin mutane da su ke aiki da kamfanin su rasa sana’arsu. Watakila kuma barin Shoprite ya taimakawa wasu kamfanonin cikan gida.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng