APC: Babu wanda ya isa ya hana Bola Tinubu takara a zaben 2023 – Babachir Lawal

APC: Babu wanda ya isa ya hana Bola Tinubu takara a zaben 2023 – Babachir Lawal

Babachir David Lawal, tsohon sakataren gwamnatin tarayya, ya ce babu wani ‘dan jam’iyyar APC da ya ke da hurumin hana Asiwaju Bola Tinubu takarar shugaban kasa a 2023.

Tun ba yau ba ake rade-radin Asiwaju Bola Tinubu zai nemi takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa. ‘Dan siyasar bai taba fitowa ya fadawa ‘yan Najeriya ya na da wannan niyya ba.

A wata hira da Mista Babachir David Lawal yayi da jaridar Punch, ya ce an ma tunbuke Adams Oshiomhole daga kujerar shugaban APC ne saboda rade-radin takarar bola Tinubu.

David Lawal ya ce wadanda su ka yi kutun-kutun wajen sauke Oshiomhole su na da burin da su ke son cinma game da ‘dan takarar APC na shugaban kasa a babban zaben 2023.

Lawal ya na mai ganin Oshiomhole bai isa ya zabi wanda zai zama ‘dan takarar APC a 2023 ba.

“Wadanda su ke so Adams Oshiohmole ya yi waje su na harin 2023 ne ido-rufe, a yadda na fahimta, a matsayinsa na shugaban jam’iyya, da wuya ya iya kakabawa jam’iyyarsa ‘dan takarar shugaban kasa.”

KU KARANTA: 2023: Na sha ban-ban da Mamman Daura - Buhari

APC: Babu wanda ya isa ya hana Bola Tinubu takara a zaben 2023 – Babachir Lawal
Babachir Lawal ya na goyon bayan takarar Bola Tinubu
Asali: UGC

Ya kuma ce: “Babu wani wanda ya ke cikin hayyacinsa a jam’iyyar APC da zai hana Tinubu damar neman kujerar shugaban kasa. Babu wani a APC da ya ke da ko da damar tare hanyarsa.”

Tun da Arewa ta yi shugaban kasa na wa’adi biyu, sai a mika damar ga yankin Kudu su fito da shugaban kasar da za ayi na gaba.”

“Asali ma me Arewa ta samu daga mulkin kasar daga tsawon shekarun da ta yi? Tun bayan mutuwar Janar Sani Abacha, aka jefa kasar cikin rashin tsaro da rashin kyawun tattali.”

“A wannan lokaci mun samu mataimakan shugaban kasa ‘Yan Arewa. Mun samu shugabannin kasa mutanen Arewa, amma saboda wasu dalilai, abubuwa ba su canzawa.” Inji Lawal.

A lokacin da ake muhawara game da yadda siyasar 2023 za ta kasance, Lawal ya na ganin cewa mulkin kasar ya zama wani nauyin kawai ne a kan wuyayan mutanen Arewa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel