Gobara ta tashi a ofishin hukumar tattara haraji ta tarayya (FIRS)

Gobara ta tashi a ofishin hukumar tattara haraji ta tarayya (FIRS)

A ranar Litinin ne wuta ta babbake sabon ginin da aka kammala a ofishin hukumar tattara haraji ta tarayya (FIRS) reshen jihar Katsina.

Gobara ta tashi a ofishin FIRS da ke kallon filin wasa na Muhammadu Dikko da misalain karfe 12:08 na ranar Litinin, kamar yadda jaridar 'The Nation' ta rawaito.

Har ya zuwa lokacin da 'The Nation' ta wallafa rahotonta, jami'an hukumar kashe gobara suna kokarin kashe wutar da ke ci a ofishin.

Kimanin makonni biyu kenan da gobara ta tashi a babban bankin Najeriya dake jihar Gombe a ranar Juma'a, 3 ga watan Yuli, 2020.

Sahara Reporters ta samu rahoto daga wata majiya cewa gobarar ta fara ci ne misalin karfe 10 na safe.

Wannan ya shiga jerin gobara da aka samu a ma'aikatun gwamnati a fadin tarayya cikin yan watannin nan.

A baya Legit.ng Hausa ta kawo muku jerin ofishoshin gwamnati biyar da suka zalzala cikin wata daya.

1. Ofishin akawunta janar (Gidan baitul mali)

A ranar 8 ga Afrilu, 2020, Ginin da aka fi sani da 'Gidan baitul mali' wato Treasury House' na kusa da hedkwatar hukumar yan sandan Abuja, a unguwar Garki ya yi gobara.

Gobara ta tashi a ofishin hukumar tattara haraji ta tarayya (FIRS)
Hedikwatar FIRS da ke Abuja
Asali: UGC

2. Hedkwatar hukumar CAC

A ranar 15 ga Afrilu, Gobara ta tashi a hedikwatar hukumar yi wa kasuwanci rijista ta kasa (CAC) da ke unguwar Maitama a birnin tarayya, Abuja.

Gobarar ta babbake hawa na karshe a ginin ofishin hukumar CAC mai bene hawa bakwai, tare da lalata muhimman kayayyaki.

DUBA WANNAN: Binciken badakala: Shugaban hukumar NDDC ya tayar da bori, ya fadi 'warwas' a gaban kwamiti

3. Hedikwatar INEC dake Abuja

A ranar 17 ga watan Afrilu, Hedkwatar hukumar gudanar da zabe ta kasa watau INEC dake birnin tarayya Abuja ya ci da wuta.

4. Ofishin babban bankin Najeriya CBN

A ranar 21 ga Afrilu, an samu gobara a ofishin babban bankin Najeriya CBN, reshen Jos, jihar Plateau. Bankin ta tabbatar da hakan a shafinta na Tuwita inda ta bayyana cewa tuni an kashe wutar.

5. Hedkwatar NIPOST

A ranar 20 ga watan Mayu, 2020, Mumunar gobara ya auku a hedkwatar hukumar ayyukan aika da karban sako watau NIPOST dake birnin tarayya Abuja.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel