Dan Agundi: Ana zargin Sarki da tsumbula masarautar Kano a harkar siyasa

Dan Agundi: Ana zargin Sarki da tsumbula masarautar Kano a harkar siyasa

- Sarkin Kano Aminu Ado Bayero zai yi wa Aminu Babba dan Agundi nadin sarauta

- Marigayi Ado Bayero ne ya cirewa Aminu Babba dan Agundi rawani a shekarar 2003

- Masanin tarihi ya ce dawo da Dan Agundi gidan dabo ya sabawa al’adar masarauta

Naɗe-naɗen da mai martaba Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya yi sun jawo abin magana. Wani masanin tarihi ya ce masarautar Kano ta tsumbula cikin harkar siyasa.

Alhaji Aminu Ado Bayero ya nada Aminu Babba dan Agundi a matsayin Sarkin Dawaki Babba wanda ya na cikin majalisar sarkin Kano. Wannan nadi ya bar baya da kura.

A shekarar 2003 ne Marigayi Ado Bayero watau mahaifin Sarki mai-ci, ya tunbukewa Babba dan Agundi rawaninsa na Sarkin Dawaki mai tuta kuma Hakimi a kasar Gabasawa.

A wancan lokaci Ado Bayero ya zargi Aminu Babba dan Agundi da rashin biyayya da shiga cikin siyasa. Tsohon Sarkin Dawakin ya shafe shekaru ya na shari’a da masarauta.

Bayan hawan Muhammadu Sanusi II kan mulki ne ya daukaka kara zuwa kotun koli inda Alkali ya tabbatar da hukuncin da Ado Bayero ya yanke, kuma masarauta ta amince da hakan.

Abin mamaki sai aka ji cewa Alhaji Aminu Ado Bayero zai yi wa Aminu Babba dan Agundi naɗin Sarkin Dawaki Babba wanda ake ke ganin an ci mutuncin fada.

KU KARANTA: Sarakan Kano da Bichi sun gana da tsohon Ciroma Sanusi Ado Bayero

Dan Agundi: Ana zargin Sarki da tsumbula masarautar Kano a harkar siyasa
Sarki Aminu Ado Bayero
Asali: Twitter

Dr. Tijjani Mohammad Naniya, Masani a jami’ar Bayero ta Kano, ya yi hira da BBC Hausa, inda ya bayyana cewa ba a taba maidawa mutum rawani bayan an cire shi daga sarauta ba.

A cewar Tijjani Mohammad Naniya, wannan mataki da sabon sarkin Kano ya dauka abin kunya ne, kuma tamkar yi wa mahaifinsa watau Sarki Ado Bayero tsirara ne.

Haka zalika Naniya ya ce da wannan al’amari an tabbatar da cewa siyasa ta shiga masarautar Kano ta yi ka-ka-gida tun daga batun tsige Sarki Muhammadu Sanusi II zuwa yanzu.

Dr. Naniya ya ce daga yanzu tarihi zai dauka cewa an dawo da wanda aka tubewa rawani cikin masarautar Kano, kuma hakan karya Daular Usmaniyya da fadar kasar Kano ne.

A baya kun ji cewa Aminu Ado Bayero zai nada yayansa, Alhaji Sanusi Ado Bayero a matsayin sabon Wamban Kano, wanda shi ma ya na cikin manyan ‘yan Majsalisar Sarki.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel