Da duminsa: An gano hannun El-Rufai, Fayemi da Amaechi a rikicin APC na Ondo

Da duminsa: An gano hannun El-Rufai, Fayemi da Amaechi a rikicin APC na Ondo

- Jam'iyyar APC reshen jihar Ondo ta zargi wasu gwamnoni biyu da wani minista da hura wutar rikicin jam'iyyar da ke aukuwar a jihar

- Gwamnonin da ake zargi sune Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti da takwaransa Mallam Nasir El-Rufai na jihar Kaduna

- Har ila yau ana zargin Rotimi Ameachi ma da hannu a wajen haddasa rikicin

Jam'iyyar APC reshen jihar Ondo ta zargi gwamnoni biyu da wani minista daya da sa hannu a rikicin jam'iyyar da ke aukuwar a jihar, jaridar The Nation ta ruwaito.

Shugaban jam'iyyar APC reshen jihar Ondo, Henry Olatuja, ya zargi gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi da takwaransa na jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai da kuma ministan sufuri, Rotimi Amaechi akan hura wutar rikicin jam'iyyar da ke balbali a jihar.

Olatuna ya ce goma daga cikin 'yan takarar kujerar gwamnan jihar na iya kin fitowa zaben fidda gwani da za a yi a ranar 20 ga watan Yuli.

Da duminsa: An gano hannun El-Rufai, Fayemi da Amaechi a rikicin APC na Ondo
Da duminsa: An gano hannun El-Rufai, Fayemi da Amaechi a rikicin APC na Ondo Hoto: The Nation
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: Shin wanene ainihin wanda aka nada rikon kwayar kujerar Magu?

Ya ce hakan za ta kasance ne idan kwamitin rikon kwarya na shugabancin jam'iyyar a matakin kasa suka nace cewa lallai sai an yi amfani da wakilai a zaben fidda gwani a jihar.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa a jiya Laraba ne aka tantance gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu.

Gwamnan na cikin 'yan jam'iyyar APC 12 da ke hankoron samun tikitin tsayawa takara a zaben gwamnan jihar da za a gudanar a ranar 10 ga watan Oktoba na 2020.

A wani sako da gwamnan jihar ya wallafa kan shafinsa na Facebook, ya yabawa mambobin kwamitin gudanarwa na jam'iyyar dangane da tsarin tantancewar da suka tanada.

Ya rubuta cewa: "Yanzu haka dai jam’iyyata ta @OfficialAPCNg ta kammala tantance ni. "Mambobin kwamitin sun kasance su na dubawa sosai, sun binciki duk wasu takardu tare da gabatar da tambayoyi. Na yi imanin cewa jam'iyyar ta tanadi tsari mai kyau."

Kwamitin riko na jam'iyyar APC na kasa dai, ya amince da tsarin amfani da wakilai a madadin 'yar tinke wajen fidda gwanin takarar gwamnan jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng