Buratai: Ba za mu huta ba sai mun tabbatar da tsaron kowa a kasar nan
Tukur Buratai, shugaban rundunar sojin Najeriya ya ce dakarun sojin kasar za su ci gaba da tsayuwa wurin yakar rashin tsaro a kasar nan har sai sun ga bayan hakan.
Buratai ya samu wakilcin laftanal janar Lamidi Adeosun a yayin bikin yaye sojoji karo na 79 a Zaria a ranar Asabar.
Shugaban rundunar sojin ya jajanta cewa Najeriya na fuskantar matsalar Boko Haram, 'yan bindiga, masu garkuwa da mutane da sauran miyagun ayyuka da ke matsantawa rayuwa.
Buratai ya taya sojojin murna tare da basu shawarar aiki tukuru, kwarin guiwa, ladabi da nagarta.
"Ina so in sanar da cewa za mu ci gaba da yakar rashin tsaron da ya addabi kasar nan," yace.
"Ana sanya ran za ku saka duk wani kwarin guiwarku wajen tabbatar da kun yi aiki cike da kwarewa.
"Ina kira gareku da ku mayar da horarwa da kuka samu ta zamo jikinku a duk inda kuka samu kanku."
Ya ce rundunar sojin ta ba baiwa dakarun abinda ya kamata sannan tana sanya ran za su yi iyakar kokarinsu a yayin ayyukansu.
KU KARANTA KUMA: Katsina: Yadda 'yan gudun hijira suka dinga kuka bayan Masari ya kai ziyara
"Akwai bukatar ku sani cewa, a yau an kara karfin rundunar sojin Najeriya saboda sun samu karuwar dakaru 4,918," yace.
"Ina tabbatar muku da cewa kun samu goyon baya daga wurinmu da kuma walwala mai dorewa."
A wani labarin kuma, mun ji ewa a kalla dakarun sojin Najeriya tara ne suka mutu a ranar Asabar sakamakon harin 'yan Boko Haram.
Mayakan kungiyar 'yan ta'addan sun halaka sojin ne bayan da suka dauki motarsu suna raka matafiya daga Maiduguri zuwa garin Damboa, wata majiya tare da jami'an tsaro suka tabbatar.
Wannan ne karo na farko da sojojin da ke raka matafiya suka fuskanci hari daga wurin mayakan.
Damboa na da nisan kilomita 85 daga kudancin Maiduguri. Ta kasance daya daga cikin kananan hukumomin da suka fi fuskantar hari daga mayakan ta'addancin a jihar Borno.
Duk da sojojin ne ke bai wa garin kariya daga 'yan ta'adda tare da tsare manyan hanyoyin, Damboa ce babbar hanyar shiga karamar hukumar Chibok a jihar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng