Cikin hotuna: Rundunar 'yan sanda ta yi bajakolin dilolin makamai da masu garkuwa da mutane

Cikin hotuna: Rundunar 'yan sanda ta yi bajakolin dilolin makamai da masu garkuwa da mutane

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta yi bajakolin wasu manyan masu laifi a hedikwatarta ta kasa da ke birnin tarayya, Abuja.

Daga cikin masu laifin da rundunar 'yan sanda ta yi bajakolinsu akwai dilolin makamai, 'yan fashi da makami da kuma masu garkuwa da mutane.

An yi bajakolin masu laifin tare da mugayen makaman da aka kama a wurinsu.

Cikin hotuna: Rundunar 'yan sanda ta yi bajakolin dilolin makamai da masu garkuwa da mutane
Rundunar 'yan sanda ta yi bajakolin dilolin makamai da sauran masu laifi
Asali: Twitter

Cikin hotuna: Rundunar 'yan sanda ta yi bajakolin dilolin makamai da masu garkuwa da mutane
Rundunar 'yan sanda ta yi bajakolin dilolin makamai da masu garkuwa da mutane
Asali: Twitter

Cikin hotuna: Rundunar 'yan sanda ta yi bajakolin dilolin makamai da masu garkuwa da mutane
Dilolin makamai da masu garkuwa da mutane da rundunar 'yan sanda ta yi bajakolinsu
Asali: Twitter

Cikin hotuna: Rundunar 'yan sanda ta yi bajakolin dilolin makamai da masu garkuwa da mutane
Rundunar 'yan sanda ta yi bajakolin dilolin makamai da masu garkuwa da mutane
Asali: Twitter

A ranar Talata ne Legit.ng ta wallafa cewa rundunar 'yan sanda a jihar Kano ta kubutar da wasu leburori fiye da 600 da aka tursasawa zama a cikin wani kamfanin sarrafa shinkafa mai suna 'popular farm rice' da ke rukunin masana'antu na Challawa a Kano.

Ma'aikatan da abin ya shafa sun shaidawa jaridar Premium Times cewa an yi musu barazanar sallama daga aiki ga duk wanda ya yi kokarin barin kamfanin domin zuwa ya gana da iyalinsa.

DUBA WANNAN: Kurunkus: Buhari ya fadi wanda ya amince da shi a matsayin shugaban APC na rikon kwarya

Jami'an rundunar 'yan sanda sun dira a kamfanin bayan samun sahalewar kotu, sun sallami ma'aikatan tare da kama manajojin kamfanin guda hudu.

A cewar ma'aikatan, an hanasu barin harabar kamfanin ne saboda tsoron kar su kwaso cutar korona daga waje idan sun fita.

Daya daga cikin ma'aikatan da aka kubutar ya shaidawa manema labarai cewa bai kara fita daga kamfanin ba tun bayan shigarsa a ranar 23 ga watan Maris.

Haruna Salihu, wani ma'aikacin kamfanin ya ce ba'a bar shi ya fita daga kamfanin ba tun bayan shigowarsa a ranar 28 ga watan Maris.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel