Yanzu-yanzu: APC ta dakatar da Aguma a matsayin mukaddashin shugaban jam'iyya

Yanzu-yanzu: APC ta dakatar da Aguma a matsayin mukaddashin shugaban jam'iyya

Rikici na sake rincabewa a jam'iyyar APC reshen jihar Ribas bayan watsi da suka yi da Igo Aguma a matsayin mukaddashin shugaban jam'iyyar na jihar.

Mambobi 28 daga cikin 38 na shugabannin ne suka ki amincewa da Aguma.

Sun amince da dakatar da Aguma a matsayin mukaddashin shugaban jam'iyyar kuma sun kafa wani kwamitin rikon kwarya wanda Sokonte Davies ya ke jagoranta.

A yayin zantawa da manema labarai a garin Fatakwal da ke jihar Ribas, mambobin kwamitin sun ce Aguma na zartar da hukunci yadda ya so tare da watsi da wasikar babbar kotun da ta nada shi shugaban jam'iyyar na rikon kwarya.

Yanzu-yanzu: APC ta dakatar da Aguma a matsayin mukaddashin shugaban jam'iyya
Yanzu-yanzu: APC ta dakatar da Aguma a matsayin mukaddashin shugaban jam’iyya Hoto: Tribune Online
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: Sauya shekar mataimakin gwamnan Ondo ya tada kura a PDP

A wani labarin kuma, mun ji cewa rikicin cikin gida na jam'iyyar APC ya raba kan gwamnoni zuwa gida biyu. Yayin da gwamnoni 13 ke goyon bayan kwamitin gudanar da ayyuka karkashin jagorancin Abiola Ajimobi, wasu gwamnoni bakwai na sukar hakan.

Bakwai daga cikin gwamonin wadanda suka kira kansu da "masu gyara" sun kosa don kwace tafiyar da jam'iyyar kafin zuwan zaben 2023.

Gwamnonin 13 sun kira bakwai din da "masu mafarki da rana tsaka.”

Wasu daga cikin masu ruwa da tsaki a jam'iyyar a halin yanzu suna bukata tare da rokon zaman lafiya.

Tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa, John Odigie-Oyegun da mataimakin sakataren jam'iyyar na kasa, Yekini Nabena sun yi kira da kawo karshen rikicin.

Tsohon mataimakin sakataren jam'iyyar, Victor Giadom na kokarin kwace shugabancin jam'iyyar.

A jiya Oshiomhole ya ce Giadom ya shirya cutar kamar yadda bangarenshi ya aikata a Ribas.

Nabena ya nuna irin wannan zargi da kushe game da Giadom.

Kamar yadda jaridar The Nation ta bayyana, gwamnoni 13 da ke goyon bayan NWC ta Ajimobi tana ganin hannun jam'iyyar PDP a cikin rikicin sannan ta dauka alkawarin shawo kan al'amarin.

Amma kuma, sauran gwamnoni bakwai din APC da basu goyon bayan Ajimobi basu damu da shugabancin jam'iyyar ba.

An gano cewa wasu daga cikin ministocin Buhari na assasa wutar al'amarin.

Majiyoyi da dama sun ce manufar wannan sashin na jam'iyyar shine gyara ta kafin zaben 2023.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel