APC: Abinda Oshiomhole ya fada a kan dakatar da shi

APC: Abinda Oshiomhole ya fada a kan dakatar da shi

Adams Oshiomhole, shugaban jam'iyyar APC da kotu ta tabbatar da dakatar da shi, ya ce zai nemi shawarar masana shari'a kafin ya sanar da mataki na gaba da zai dauka.

Oshiomhole ya bayyana hakan ne ga gidan talabijin na Channels yayin da suka tuntube shi domin jin ta bakinsa dangane da tabbatar da dakatar da shi da wata kotun daukaka kara ta yi.

Idan za ku tuna kotun daukaka kara da ke Abuja ta jaddada dakatar da Adams Oshiomhole a matsayin shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

A ranar 4 ga watan Maris ne wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta amince da bukatar wasu mambobin APC shida na jihar Edo wajen dakatar da Oshiomhole.

Darakta Janar na Voice of Nigeria (VON), Osita Okechukwu, ya bayyana dakatar da shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole da kotun daukaka kara tayi a matsayin babban kwanciyar hankali ga jam’iyyar.

Wannan na zuwa ne bayan Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya ce ya amince zai taimaki takwaransa na jihar Edo, Godwin Obaseki, don koyawa Oshiomhole darasi a jihar.

APC: Abinda Oshiomhole ya fada a kan dakatar da shi
Oshiomhole
Asali: UGC

Na amince zan taimaki Obaseki don koya wa Oshiomhole darasi a jihar Edo. Oshiomhole ya koma ya tambayi Amechi yadda muka kare,” Wike ya wallafa a shafinsa na Twitter a jiya Talata.

Yanzu haka rikicin shugabanci da ake yi a jami'yyar All Progressives Congress, APC, mai mulki ya dauki sabon salo yayin da kwamitin zartarwa na jami'yyar ta sake jadada Abiola Ajimobi a matsayin shugaban riko.

Uwar jam'iyyar ta yi watsi da Victor Giadom, wanda ya bayyana kansa matsayin shugaba.

DUBA WANNAN: Rotimi Akeredolu ya ziyarci Buhari da fom dinsa na takarar gwamna

Jam'iyyar ta ce Giadom baya cikin 'yan kwamitin zartarwar tun lokacin da ya yi murabus daga mukaminsa na mataimakin babban sakatare domin ya yi takarar kujerar mataimakin gwamna a jihar Rivers.

Kafin nadinsa Ajimobi ne mataimakin shugaban jamiyya na kasa na shiyar Kudu.

APC ta jadada shugabancin Ajimobi ne yayin taron gaggawa karo na 45 da ta kira wanda ya samu hallarcin mutum 15 cikin mambobi 21 na NWC.

Hillary Eta wanda aka zaba domin jagorantar taron ya sanar da kafa kwamitin mutum bakwai da za su gudanar da zaben fid da gwani na gwaman jihar Edo da za ayi ranar 22 ga watan Yuni.

Gwamna Hope Uzodima na jihar Imo ne zai jagoranci kwamitin yayin da Sanata Ajibola Bashiru zai yi aiki a matsayin sakataren kwamitin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel