Buhari ya amince da fitar da N123bn don gina layin dogo daga Ibadan zuwa Kano

Buhari ya amince da fitar da N123bn don gina layin dogo daga Ibadan zuwa Kano

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da biyan N123 biliyan don aikin titin jirgin kasa daga Ibadan zuwa Kano.

Ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya bayyana cewa akwai yuwuwar a fara aikin titin jirgin kasan zuwa karshen watan Augusta.

Aikin, wanda gwamnatin kasar China ta dauka nauyi zai ci $5.3 biliyan. Kamfanin China Civil Engineering and Construction Corporation ne zai yi aikin.

Amaechi, wanda ya sanar da hakan a tattaunawar da aka yi da shi a gidan talabijin din Channels a ranar Damokaradiyya, ya jinjinawa gwamnatin kasar China wacce yace tana matukar taimako wurin mayar da titunan jiragen kasa na tarayya zuwa na zamani.

Ya ce majalisar zartarwa ta tarayya ta amince da bude asusun da za a dinga saka ribar da aka samu daga ayyukan jiragen kasan don biyan gwamnatin kasar China.

Buhari ya amince da fitar da N123bn na titin jirgin kasa daga Ibadan zuwa Kano
Buhari ya amince da fitar da N123bn na titin jirgin kasa daga Ibadan zuwa Kano. Hoto daga Daily Trust
Asali: Facebook

KU KARANTA: 'Yan Najeriya miliyan 39.4 na iya rasa ayyukansu kafin karshen shekara - FG

Amaechi ya kara da cewa, an fara diban fasinja 300 ne a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna amma a yanzu sama da fasinja 4,000 ake diba a kowacce rana.

Ya ce a lokacin da jirgin kasan ya fara aiki, gwamnati na asarar N46 miliyan a kowanne wata, amma a yanzu ana samun ribar N109 miliyan zuwa N110 miliyan a kowanne wata.

Amaechi ya kara da cewa, a lokacin da jiragen kasan Ibadan zuwa Kano za su fara aiki tare da taragon daukar kaya, za a samu riba mai tarin yawa da za ta kawo sassauci wurin biyan bashin da aka ci.

Ya ce: "Dole ne mu alakanta nasarar titunan jiragen kasan Najeriya da shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari."

A wani labari na daban, gwamnatin tarayyar ta yi bayyana cewa mudin ba a dauki mataki cikin gaggawa ba, a kalla 'yan Najeriya miliyan 39.4 suna iya rasa ayyukansu sakamakon tsaikon da annobar COVID-19 ta yi a kasar.

Ta kuma bayyana fargabatar ta kan yiwuwar miliyoyin yan Najeriya za su fada cikin halin matsanancin talauci kafin annobar ta wuce.

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ne ya yi wannan jawabin a ranar Alhamis yayin da ya ke gabatar da jawabin kwamitin tattalin arziki ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel