Hamza Al-Mustapha ya yi fashin baki game da dukiyar da ake cewa Abacha ya sace
Tsohon jami’in tsaron da ke kula da tsohon shugaban kasa Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha, ya tashi ya sake kare mai gidansa a game da zargin da ake yi masa na satar dukiyar gwamnati.
Hamza Al-Mustapha ya ce gwamnatin Sani Abacha ta tuntubi sarakunan Arewa da na Kudu da duk wasu manya da ake ji da su a Najeriya kafin gwamnati ta boye biliyoyin kudin da yanzu ake kira ‘satar Abacha.’
Al-Mustapha ya bayyana haka ne a lokacin da ya zanta da gidan jaridar BBC Hausa, inda ya ce dole ta sa Janar Sani Abacha ya rika boye biliyoyin kudi a kasar waje domin ya hararo cewa za a makawa Najeriya takunkumi.
“A dalilin wannan takunkumi ne Abacha ya boye kudin kasar a ketare saboda ka da ‘yan Najeriya su shiga cikin matsala.”
Game da wannan kudi da ake maganarsa a yau, Hamza Al-Mustapha ya ce: “Mun tara Sarakunan Arewa da na Kudu, tare da manyan da ke cikin gwamnati da wadanda ba su ciki a wancan lokaci.”
“Shawara ce wanda aka dauka bayan an yi taron masu ruwa da tsaki da sarakunan gargajiya na fadin Najeriya.”
Al-Mustapha ya ke cewa: “Ina fadan wannan ne saboda abin da na sani da kuma amana ga ‘yan Najeriya.”
KU KATANTA: Al-Mustapha: Tarihin babban Dogarin tsohon Sani Abacha
“Mun hadu ne a wani wuri da ake kira Camp Bassey officer’s mess a fadar shugaban kasa. A nan ne mu ka tattauna game da barazanar makawa Najeriya takunkumi, an ci ma matakai da dama.”
“Ministan kudi, da ministan tsare-tsaren kasafin kudi da irinsu gwamnan babban bankin kasa na CBN sun halarci wannan taro.”
Dogarin na marigayi Sani Abacha ya ke cewa akwai ban mamaki a rika cewa wannan kudi na Abacha ne bayan babu hujjar da ke nuna sa hannunsa ko hotonsa a bankunan da aka ajiye kudin.
“Ina mamakin yadda ake cin zarafin Abacha.”
“Lokacin da ya karbi mulki, kudin kasar wajen Najeriya bai kai dala biliyan biyu ba, abubuwa babu tsari.”
Ya ce: "A shekara hudu da watanni takwas, kudin su ka koma Dala biliyan tara.”
“Watanni tara da mutuwar Abacha wannan kudi su ka bi iska. Har yau wadanda su ka sace wannan kudi su na nan, babu yadda aka yi da su."
Sojan ya ce sau takwas ana yunkurin kifar da gwamnatin Abacha, amma mutane labarin juyin mulki uku kurum su ka sani. "Har lokacin da Abacha ya mutu, wasu na kitsa masa juyin mulki."
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng