Kaduna: An kashe matasa 4 da ake zargi da zama 'yan leken asiri

Kaduna: An kashe matasa 4 da ake zargi da zama 'yan leken asiri

Sakamakon ci gaban fadan kabilanci tsakanin kabilar Adara da Fulani a yankin karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna, Daily Trust ta gano cewa an kashe matasa 4 'yan kabilar Adara a ranar Asabar.

'Yan uwansu ne suka konesu a kauyukan Doka sa Kallah da ke karamar hukumar Kajurun sakamakon zarginsu da suka yi da kaiwa Fulani bayanai a kansu.

An gano cewa, an banka wa Danladi Shekarau sa David Kampani wuta a kauyen Doka bayan an zargesu da yin fuska biyu yayin da aka kashe Jumare Anthony a kauyen Kallah duk a kan zargi daya.

Majiya daga Doka ta tabbatar da cewa hankali ya matukar tashi a yankin. An gano su ne sakamakon kama daya daga cikin mamatan da aka yi yana tallafa wa Fulani bankawa wasu sassan kauyen wuta bayan sun kai hari a makon da ya gabata.

Kaduna: An kashe matasa 4 da ake zargi da zama 'yan leken asiri
Kaduna: An kashe matasa 4 da ake zargi da zama 'yan leken asiri Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

Majiyar wacce take da alaka da daya daga cikin mamatan, ta ce: "An banka musu wuta ne sakamakon zarginsu da ake yi da zama 'yan leken asirin Fulani.

"Ba mu ji dadin rashin adalcin da aka yi wa 'yan uwanmu ba da sauran wadanda abun ya ritsa da su.

"Dukkansu jakadun zaman lafiya ne kuma masu bin doka ne a karamar hukumar Kajuru da jihar Kaduna baki daya," yace.

A ranar Litinin ne rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta kama mutum biyar da ake zargi da sa hannunsu a kisan matasa hudu na karamar hukumar Kajurun.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, ASP Mohammed Jalige, yayin tabbatar da kisan matasan ya ce wadanda aka kama a halin yanzu suna hannun 'yan sanda.

KU KARANTA KUMA: Zamfara: Sojin sama sun ragargaza maboyar 'Dogo Dede' shugaban 'yan bindiga (Bidiyo)

A yayin da aka tuntubi shugaban kungiyar cigaban Adara, Dio Maisamari, ya sanar da Daily Trust cewa an sanar da shi aukuwar lamarin kuma kungiyarsa ta yi Alla-wadai da faruwar al'amarin.

A wani labarin kuma, Legit.ng ta rahoto a baya cewa 'yan bindiga sun yi garkuwa da shugaban kotun gargajiya, Mai shari'a Donatus Yantau Shidda a jihar Taraba.

An sace babban alkalin ne a safiyar yau Litinin a jihar Taraba.

Wata majiya daga iyalansa ta ce Shidda na tare da matarsa a yayin da 'yan bindigar suka isa gidansa da ke yankin Kona a Jalingo.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng