Biyan bashi: FG za ta rabawa wasu jihohi biyar biliyan N148
- Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya amince da bukatar neman a rabawa wasu jihohi biyar fiye da biliyan N148
- Za a rabawa jihohin kudin ne a matsayin biyan bashin kudaden da suka kashe domin gyaran hanyoyin gwamnatin tarayya a jihohinsu
- Majalisar zartawa ta tarayya (FEC) ta yi gargadin cewa daga yanzu ba zata kara biyan wata jiha bashin kudin gyaran hayoyin tarayya ba matukar ba izinin yin hakan ta samu ba daga FG
Majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) ta amice da biyan wasu jihohi biyar jimillar N148,141,987,161.25 a matsayin biyan bashin kudaden da suka kashe wajen gyaran hanyoyin gwamnatin tarayya a jihohinsu.
Da ya ke sanar da hakan ga manema labarai a fadar shugaban kasa, ministan yada labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed, ya ce ministan aiyuka da gidaje, Babatunde Fashola, ne ya gabatar da kudirin neman biyan jihohin.
Jihohin da FEC ta amince za a biya kudin sune kamar haka; Kuros Riba, Ondo, Osun, Bayelsa da Ribas.
FEC ta amice da biyan jihohin adadin kudin yayin zamanta na mako - mako da ta saba gudanarwa kowacce ranar Laraba.
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ne ya jagoaranci taron FEC da aka yi ranar Laraba da ta gabata. An gudanar da taron ne ta hanyar fasahar zamani mai amfani da yanar gizo.
DUBA WANNAN: Kwadayin kujerar gwamna: Mataimakin gwamnan APC ya kammala shirin komawa PDP a cikin sati mai zuwa
Kasafin kudin ya nuna cewa jihar Kuros Riba zata samu jimillar N18,394,737,608.85, jihar Ondo N7,822,147,577.08, jihar Osun N2,468,938,876.78, jihar Bayelsa N38,040,564.40, jihar Ribas N78,953,067,518.29.
Sai dai, ministan ya bayyana cewa wannan shine karo na karshe da FG zata biya wata jiha irin wannan bashi.
Ya kara da cewa daga yanzu FG ba zata biya wata jiha bashin kudin gyran hanyoyin tarayya ba matukar ba FG ce ta bata izinin yin hakan ba.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng