Boko Haram: A karo Dakarun sojoji 100, 000 a Najeriya – Kwamitin Majalisa

Boko Haram: A karo Dakarun sojoji 100, 000 a Najeriya – Kwamitin Majalisa

Majalisar wakilan tarayya ta yi kira ga jami’an tsaron Najeriya su kara daukar sojoji 100, 000 domin a rufe gibin da ake da shi na rashin isassun dakaru wajen yaki da ta’addanci.

‘Yan majalisar wakilan kasar sun yi kira da cewa a kara yawan sojoji a Najeriya. Majalisar ta ce wannan zai taimaka wajen samun nasara a yakin da ake yi da tsageru da ‘yan ta’adda.

Bayan haka majalisar ta nemi sojojin kasa su dawo da jami’an da su ka yi ritaya, a ajiye su idan bukata ta tashi. Wannan ya na cikin sashe na 25 a kashi na 7 na dokokin gidan soja.

‘Yan majalisar sun bada sharadin cewa ka da sojojin da za a maido aiki su zarce shekaru 50, sannan kuma su zama cikin koshin lafiya da karfin jiki ta yadda za su iya yin amfani a yaki.

Wannan kira ya zo ne daga bakin kwamitin majalisar wakilai a kan harkar sojojin kasa bayan kwamitin ya yi bincike game da harin da Boko Haram ta kai kwanaki a garin Auno.

KU KARANTA: Matsaloli biyu da mu ke fama da su a Najeriya - Ministan tsaro

Boko Haram: A karo Dakarun sojoji 100, 000 a Najeriya – Kwamitin Majalisa
Shugban Majalisar Wakilai Hoto: Twitter/HouseNgr
Asali: Facebook

Shugaban wannan kwamiti da ke kula da sojojin kasa, Honarabul Abdulrazak Namdaz ne ya gabatar da rahoton binciken kwamitin a zauren majalisa a zaman farko na makon nan.

Da ya ke magana game da mummunan harin da aka kai a Auno, Abdulrazak Namdaz ya ce jami’an tsaro ba su bada isasshen kariya ga matafiyan da su ka fada hannun ‘yan ta’ddan ba.

Namdaz ya ke cewa an samu matsala ne: “Saboda sojojin kasa ba su da isassun dakarun da za su rike wuta na tsawon lokaci bayan sun lallasa ‘yan Boko Haram a wasu kauyuka.”

“Wannan ya sa ake tarwatsa rundunar sojin domin a kafa tawaga mai karfi. Idan har aka dauki sojoji rututu aiki, babu bukatar a rika kafa wata tawaga ta musamman” inji Namdaz.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel