Boko Haram: Majalisar wakilai ta gano tushen har Auno, ta bukaci diban karin dakarun soji

Boko Haram: Majalisar wakilai ta gano tushen har Auno, ta bukaci diban karin dakarun soji

Majalisar wakilan Najeriya ta yi kira ga hukumomin rundunar sojin kasar nan da su dauki karin dakaru 100,000 na soji don maye gurbin rashin sojin da kasar nan ke fama dashi don kawo karshen kalubalen tsaro.

Sun kara kira ga rundunar sojin kasar nan da ta kira jami'anta da suka yi murabus matukar suna da lafiya kuma basu wuce shekaru 50 ba kamar yadda bangare na VII, sashi na 25 ya amince.

Wannan na daga cikin kira da kwamitin majalisar mai bincikar kisan Auno da ta faru a watan Fabrairu suka yi.

Shugaban kwamitin kula da rundunar soji, Abdulrazak Namdaz, wanda ya mika rahoton gaban majalisar, ya ce ba a ba matafiya wani tsaro ta hanyar saka sojin a kan babbar hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.

Boko Haram: Majalisar wakilai ta gano tushen har Auno, ta bukaci diban karin dakarun soji
Boko Haram: Majalisar wakilai ta gano tushen har Auno, ta bukaci diban karin dakarun soji Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

A yayin mika rahoto, Namdaz ya ce bincikensu ya bankado cewa matafiya ne aka tare a kauyen Auno bayan sun ki bin dokar hana walwala da aka saka a kauyen, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce wannan lamarin ne yasa mayakan Boko Haram suka samu damar halaka mutane birjik.

"A dayan bangaren kuma, da sojojin sun bai wa matafiyan kariya, da ba a rasa rayuka masu yawan hakan ba.

"Da kuma an yi nasarar kama wa ko kashe wasu daga cikin 'yan ta'addan ba tare da an samu yawan mamata a cikin matafiyan ba.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya maye gurbin mamacin da ya nada a hukumar FCC

"Hakan ya faru ne saboda rundunar sojin bata da jami'ai masu yawa da za su iya kai mayakan ta'addancin kasa a wasu kauyukan, shiyasa dakarun marasa yawa ake cin galabarsu.

"Ta hanyar diban sojoji, za a maye wannan gurbin na rashin ma'aikata."

A wani labarin na daban, majalisar wakilan tarayya ta amincewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, karban bashin $22.7bn daga kasar waje.

Yan majalisar sun amince da karbo bashin ne a zaman majalisan da ya gudana ranar Talata bayan samun rahoton kwamitin basussuka.

Za ku tuna cewa lokacin da shugaba Buhari ya mika bukatar karban bashin a 2019, ya ce za'ayi amfani da su wajen wasu manyan ayyuka don jin dadin al'umma.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel