'Yan bindiga sun budewa shugaban jam'iyyar APC wuta yayin da ya ziyarci kauyensu a Katsina

'Yan bindiga sun budewa shugaban jam'iyyar APC wuta yayin da ya ziyarci kauyensu a Katsina

'Yan bindiga a jihar Katsina sun kashe shugaban jam'iyyar APC na karamar hukumar Batsari, Abdulhamid Sani Ruma, a kauyensu.

Ruma ya gamu da ajalinsa ne yayin da ya ziyarci kauyensu, Sabon Garin Dunburawa, domin jagorantar rabon gado ga 'ya'yan dan uwansa da 'yan bindiga su ka kashe a shekarar da ta gabata.

Wata majiya ta sanar da Daily Trust cewa wasu 'yan bindiga ne a kan babura, da su ka fito daga jeji, su ka da budewa Ruma wuta, inda ya mutu nan take.

Likitoci sun tabbatar da mutuwarsa bayan an kai gawarsa babban asibitin karamar hukmar Batsari

"Ya bar kauyen nan da misalin karfe 9:00 na safe domin komawa gidansa da ke garin Batsari. Kilomita hudu ne daga kauyen Sabon Garin Dunburawa zuwa garin Batsari.

"Shi kadai aka harbe a cikin mutanen da su ke tare," a cewar majiyar Daily Trust.

Mataimakin shugaban jam'iyyar APC na mazabar Katsina ta tsakiya, Mamman Yaro Batsari, ya tabbatar da kisan Ruma.

Ya ce batun kisan Ruma da 'yan bindigar su ka yi, ya jefa jama'a cikin firgici.

"A irin wannan lokacin 'yan bindiga su ka kashe dan uwansa shekarar da ta gabata, yanzu kuma shi ma su ka kashe shi bayan ya ziyarci kauyensu domin rabon gadon dan uwan nasa da aka kashe

"Ya na cikin gonaki yayin rabon gadon ne sai wasu 'yan bindiga su ka bullo daga cikin jeji su ka bude ma sa wuta.

'Yan bindiga sun budewa shugaban jam'iyyar APC wuta yayin da ya ziyarci kauyensu a Katsina
'Yan bindiga sun budewa shugaban jam'iyyar APC wuta yayin da ya ziyarci kauyensu a Katsina
Asali: UGC

"Shi kadai su ka harba, sun harbe shi a ka da kirji. Yanzu haka an dauki gawarsa zuwa gidansa domin yi ma sa jana'iza," a cewarsa.

Har ya zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, rundunar 'yan sandan jihar Katsina ba ta ce komai ba a kan faruwar lamarin.

DUBA WANNANAN: Yadda tsohon gwamnan APC ya dinga biyan kansa alawus din N50m duk bulaguro zuwa Abuja

A wasu hare - haren 'Yan bindiga sun kashe mutane uku a kauyen Matseri da ke yankin karamar hukumar Faskari a jihar Katsina.

Yayin harin da 'yan bindigar su ka kai a daren ranar Asabar, sun raunata karin wasu mutane 6 tare da lalata dukiyar jama'a.

A cewar mazauna yankin, 'yan bingar sun kai hare - hare a kan babura a kauyuka uku da su ka hada da Yan Nasarawa, Unguwar Alhaji Babba, da Unguwar Kanya a karamar hukumar Faskari.

Mazauna yankin sun ce 'yan bindigar sun yi awon gaba da dabbobin jama'a a kauyukan da su ka kai hare - haren.

Sai dai, da gidan talabijin na Channels ya tuntubi, SP Gambo Isah, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina, ya ce labarin kai hare - haren bai zo ma sa ba.

Mazauna kauyukan sun bayyana cewa sun binne jama'ar da aka kashe yayin da wadanda su ka samu raunuku ke cigaba da samun kulawa.

Harin na zuwa ne bayan kwana daya kacal da kashe mutane 13 a wani hari da 'yan bindigar su ka kai a kauyukan Unguwar Gizo, Maigora, Sabon Layi, da Mai Ruwa a karamar hukumar Faskari.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel