Majalisa ta jefa kwangilolin cuwa-cuwa a kasafin NDDC – Kemebradikumo Pondei

Majalisa ta jefa kwangilolin cuwa-cuwa a kasafin NDDC – Kemebradikumo Pondei

- Shugaban NDDC, Kemebradikumo Pondei ya ce an yi cushe a kasafin hukumarsa

- Pondei ya zargi majalisa da yin cushen ayyukan bogi a cikin kasafin kudin NDDC

Shugaban hukumar NDDC na rikon kwarya, Farfesa Kemebradikumo Pondei, ya jefi ‘yan majalisar tarayya da zargin yin cushe a cikin kasafin kudin NDDC na shekarar bara watau 2019.

Kemebradikumo Pondei ya fadawa manema labarai cewa an cusa kwangilolin bogi kusan 500 a kasafin 2019. Pondei ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 26 ga watan Mayu, 2020.

Farfesa Pondei ya bayyanawa ‘yan jarida wannan ne a jihar Ribas, a matsayin martani game da zargin da ake yi wa shugabannin rikon kwaryar NDDC na yin awon gaba da kudi.

Shugaban na NDDC ya ke cewa sun gano ta’adin ne lokacin da su ka binciki kasafin kudin hukumar na 2019. Pondei ya ce ‘yan majalisa sun jirkita kasafin da aka aika masu.

“Mun gano cewa bayan hukumar ta aikawa kwamitin NDDC a majalisar tarayya, ba mu iya gane kundin kasafin kudin da aka dawo mana da shi ba.” Inji Kemebradikumo Pondei.

KU KARANTA: Abin da ya jawo rigimar Ministan sadarwa da Shugaban hukumar ci-rani

Majalisa ta jefa kwangilolin cuwa-cuwa a kasafin NDDC – Kemebradikumo Pondei
Shugaban NDDC na rikon kwarya Kemebradikumo Pondei Hoto: The Cable
Asali: UGC

“An yi wa kasafin kudin 2019 wani irin cushen hauka, inda aka lafta sababbin ayyuka kusan 500 aka dawo mana da su. Mun gano cewa an warewa muhimman ayyukan kudi kadan.”

Idan ba ku manta ba shugaba Muhammadu Buhari ya bada umarnin a binciki kudin da aka kashe a hukumar NDDC. Wannan zai sa a bankado duk barnar da jami’an hukumar su ka yi.

Sai dai shugaban hukumar mai kula da cigaban Neja-Delta, Farfesa Pondei ya ce babu wani kwangilar kirki da NDDC ta yi. Pondei ya ce an bar hukumar da 'yan kananan ayyuka.

Pondei ya nuna takaicinsa game da yadda aka bar hukumar NDDC ta koma gina hanyar ruwa, da kafa karafunan wuta, abin da a cewarsa ko karamar hukuma za ta iya daukar nauyi.

A jawabin da ya yi wa ‘yan jarida, farfesan ya ce wadanda su ke tsoron binciken kudin da shugaban kasa ya ce ayi ne su ke zargin kwamitin rikon kwaryarsa da cin kudin hukuma.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel