Yanzu Yanzu: An saki babban jami’in soja da wasu biyu da aka sace
- Masu garkuwa da mutane sun sako hafsin sojan da suka sace a jihar Ondo
- An sako sojan ne tare da wasu mutum biyu a daren Laraba a garin da ke tsakanin iyakar jihohin Ondo da Edo
- Kakakin rundunar soja ta 32 da ke barikin Owena ta Akure, ya tabbatar da sakin sojan a safiyar Alhamis
Masu garkuwa da mutane sun sako hafsin sojan da suka sace a jihar Ondo, SaharaReporters ta ruwaito.
An sako sojan ne tare da wasu mutum biyu a daren Laraba a garin da ke tsakanin iyakar jihohin Ondo da Edo.
Kaftin Ayorinde Omojokun, kakakin rundunar soja ta 32 da ke barikin Owena ta Akure, ya tabbatar da sakin sojan a safiyar Alhamis.
Ya ce a halin yanzu hafsin sojan yana kan hanyar sa ta zuwa Ibadan da ke jihar Oyo.
A baya mun ji cewa wasu 'yan bindiga sun yi garkuwa da wani sojan Najeriya a kan hanyar Auga zuwa Akoko da ke karamar hukumar Akoko ta arewa maso gabas ta jihar Ondo.
An gano cewa sojan na tafiya ne shi kadai a cikin motarsa yayin da 'yan bindigar suka damke shi tare da shigewa daji da shi.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Ondo, ASP Tee-Leo Ikoro ya tabbatar da aukuwar lamarin ga gidan talabijin din Channels.
Ya ce sojan da aka sace ya kai mukamin kaftin wato mai anini uku kenan.
KU KARANTA KUMA: Sabon sautin murya: Muhimman sakonni 5 da Shekau ya fitar
Yana kan hanyarsa ta zuwa Abuja daga Ibadan yayin da 'yan bindigar suka sace shi a Auga Akoko.
"Sun shigar da shi daji amma sun ba shi damar waya da 'yan uwansa wadanda suka garzaya tare da sanar da ofishin 'yan sanda da ke yankin Ikare-Akoko.
"Amma kuma abun takaicin shine yadda kafin 'yan sanda su isa yankin, 'yan bindigar sun sauya mishi wuri. An samu motarsa da suka bari a wurin."
Ikoro ya jaddada cewa kwamishinan 'yan sandan jihar, Undie Adie ya bada umarnin yin bincike sosai don ceto Kaftin Gana.
Ya yi kira ga 'yan jihar masu matukar kare dokokin da kada su tsorata don za su samu isasshen tsaron rayukansu da dukiyoyinsu.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng