Korona: Ta harbi karin mutane 248 a Najeriya, jimilla 4399, ta hallaka mutum 143, 773 sun warke

Korona: Ta harbi karin mutane 248 a Najeriya, jimilla 4399, ta hallaka mutum 143, 773 sun warke

Hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa a kasa (NCDC) ta ce annobar cutar covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 248 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da NCDC ta fitar da misalin karfe 11:20 na yammacin ranar Lahadi, 10 ga watan Mayu, 2020.

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na tuwita, ta sanar da cewa karin sabbin mutane 239 din sun fito daga jihohin Najeriya kamar haka;

81-Lagos

35-Jigawa

26-Borno

26-Kano

20-Bauchi

13-FCT

12-Edo

10-Sokoto

7-Zamfara

4-Kwara

4-Kebbi

2-Gombe

2-Taraba

2-Ogun

2-Ekiti

1-Osun

1-Bayelsa

NCDC ta ce ya zuwa karfe 11:20 na yammacin ranar Lahadi, 10 ga watan Mayu, akwai jimillar mutane 4399 da aka tabbatar da cewa suna dauke da kwayar cutar covid-19 a fadin Najeriya.

An sallami mutane 778 bayan an tabbatar da sun warke sarai, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 143.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel