Ba zan daina kukan rashin Ubale ba – Yakubu Muhammed ya yi zantuka masu taba zuciya kan marigayin

Ba zan daina kukan rashin Ubale ba – Yakubu Muhammed ya yi zantuka masu taba zuciya kan marigayin

Fitaccen jarumin Kannywood Yakubu Muhammed, ya nuna alhini a kan rasuwar abokin aikinsa kuma amininsa, Ubale Ibrahim.

Muhammed ya bayyana cewa shakka babu sun yi babban rashi, inda ya ce ya kasa tsayar da hawayen da ke kwaranya a idanunsa a kan wannan lamari.

Jarumin ya kara da cewar ko a jiya Alhamis, 30 ga watan Afrilu, kafin rasuwansa, sun yi waya da marigayin bayan an sha ruwa na azumin Ramadana, inda suka yi za su hadu da safe.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Allah ya yi wa wani dan majalisar dokokin jahar Nasarawa rasuwa

Ga yadda ya wallafa a shafinsa na Instagram:

“Ubale(Auwal) Ibrahim: Allah ya ji kan ka Ubale. Mun yi babban rashi. Muna bude baki ya kira ni, muka yi magana akan da safe zamu hadu.

“Yayi sallar Isha,sun ci abinci da abokan sa a unguwar su, ya yanke jiki ya fadi,ashe tafiyar kenan. Mai dakin sa ta kira mu sai asibiti, muna isa Doctors suka ce ai ya rasu. Innalillahi wa inna ilayhir raji'un.

“Ubale ya girme mu ni da Sani amma ya kasance a sana'ance a kamfanin mu yake. Duk abinda ka sa shi ba girman kai ba dagawa zai je yayi. Wanda bai kai shi ba ma sai ka ga yasa Ubale aiki ko kuma kaga ya aike shi kuma kaga yaje.

“Ubale a wajen marigayiya mahaifiyar Sani Danja ya girma,duk da ba 'yanuwantaka na jini,unguwace kawai ta hada su, sai da ya zama kamar ita ta haife shi .

"Idan aka nemi Sani ko Yakubu bama nan, Toh Ubale shine wakilin mu. A dawainiyar mu bai taba nuna gazawa ko kosawa ba. Yayi dawainiya damu da 'ya'yan mu.

“Duk inda naje Ina shigowa Kano shi nake fara kira awaya. Ya girme ni amma Yallabai yake cemin. Sai ka ka ji yace 'Yallabai gani nan zuwa' Komai yake zai bari ya zo inda nake.

"Dole ne in yi kuka, Ubale ya sha wahala sosai. Last year daidai wannan lokacin(azumin bara) Hawan Jinin sa ya tashi har sai da yayi Loosing Memory for over a month, ba ya iya gane komai, hatta iyalin sa da 'ya'yan sa.

“Muka yi ta magani har Allah ya bashi lafiya .Sau tari bashi da kudi, babu abinci da za su ci a gidan sa,amma bazai taba bude baki yace ga halin da gidan sa yake ciki ba ,sai dai in mun lura da yanayin sa mun tambaye shi sannan zai fada mana a magance masa matsalar.

“Bai damu da abin duniya ba .Idan na dame shi da bai son kazar-kazar wajen neman kudi sai ya kalle ni yayi murmushi yace Yakubu kenan...He was always comfortable with the little da ya samu.

"Ubale kwalliya da Riga basu dame shi ba. Idan yayi wata shigar sai na yi ta masa surutu ince kai fa actor ne, television star, ya kamata ka dinga yin gayu sai yayi dariya yace Yakubu kenan.

“Ko Ubale yayi fushi lokaci kankani zaka ga ya huce komai ya wuce. Haihuwar sa na farko yayi min takwara. Yasa wa jariri Yakubu. Yakubu is now 17 years old about to go to University. RIJF Ubale."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel