An Fara Shirin Nemo Kuri'u Miliyan 20 ga Shugaba Tinubu a Zaben 2027

An Fara Shirin Nemo Kuri'u Miliyan 20 ga Shugaba Tinubu a Zaben 2027

  • Ƙungiyar Tinubu Again Movement da Bello Matawalle ke jagoranta ta ce ta yi rajistar magoya baya sama da miliyan 1.23 a faɗin Najeriya
  • Ƙungiyar ta ce yankin Arewa maso Yamma ne cibiyarta mafi ƙarfi, inda ta samu mambobi sama da 300,000
  • Ta sanya burin tara masu zaɓe da magoya baya miliyan 20 domin sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu a shekarar 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Sokoto - Wata ƙungiyar siyasa mai suna Tinubu Again Movement, wadda Ministan Tsaron Ƙasa mai kula da harkokin tsaro, Bello Matawalle, ke jagoranta, ta ce ta yi rajistar magoya baya sama da miliyan 1.23 a faɗin Najeriya.

Ƙungiyar ta kuma bayyana cewa tana da burin tara masu zaɓe da magoya baya miliyan 20 domin ganin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake lashe zaɓen shugaban ƙasa a shekarar 2027.

Kara karanta wannan

Matashin dan APC ya kama sunan Buhari, ya fadi rashin kyautawar da ya yi sa Tinubu a 2023

Za a nemo kuri'u ga Tinubu
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Darakta mai kula da yaɗa labarai da sadarwa na ƙungiyar, Yusuf Dingyadi, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya bai wa jaridar The Punch a Sokoto ranar Alhamis, 12 ga watan Nuwamban 2026.

Kungiyar ta ce yankin Arewa maso Yamma ne cibiyarta mafi ƙarfi wajen wayar da kan jama’a da tattara magoya baya, inda ta samu mambobi sama da 300,000.

Dingyadi, wanda kuma shi ne babban mataimaki na musamman kan harkokin yaɗa labarai ga shugaban APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, ya ce ƙungiyar ta ƙara ƙaimi wajen gudanar da kamfen a matakin ƙananan hukumomi da al’ummomi.

Abin da kungiyar ta mayar da hankali a kai

Ya bayyana cewa kamfen ɗin na ƙara samun karɓuwa musamman a yankunan karkara, inda masu aikin sa-kai ke tattaunawa da mazauna yankunan kan ayyuka da manufofin gwamnatin Tinubu.

A cewarsa, ƙungiyar na amfani da ayyukan da gwamnatin ta gudanar a fannin samar da ababen more rayuwa da sauran sassa domin shawo kan ’yan Najeriya su goyi bayan wa’adin mulkin Tinubu na biyu.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Wike zai raba biliyoyi don tabbatar da tazarcen Tinubu

Dingyadi ya ce:

“Shugaba Asiwaju Bola Ahmed Tinubu yana da abubuwan da zai nuna wa jama’a, waɗanda za a iya tallatawa ba tare da fargabar wani ya musanta su ba.
“Dangane da bunƙasa ababen more rayuwa, akwai ayyuka da dama. Muna zagayawa domin wayar da kan mutane da sanar da su abubuwan da shugaban ƙasa ya yi da kuma waɗanda yake ci gaba da yi.”

Jihohin da ƙungiyar ta samu mambobi

A cewar Dingyadi, ƙungiyar ta samu gagarumin goyon baya a jihohin Sokoto, Kebbi, Zamfara, Katsina, Kano, Jigawa da Kaduna.

Ya ƙara da cewa an tattaro masu aikin sa-kai sama da 5,600 daga ƙungiyoyi da dama masu goyon bayan APC, da wasu ƙungiyoyi da ƙungiyoyin haɗin gwiwa a faɗin Arewa maso Yamma.

Hakazalika, ya ce an tattara waɗannan masu aikin sa-kai ne domin faɗaɗa yaɗuwar kamfen ɗin da ƙara yawan mutanen da ƙungiyar za ta iya isa gare su.

Dingyadi ya jaddada cewa burin ƙungiyar shi ne samun masu zaɓe da magoya baya miliyan 20 a faɗin ƙasar nan domin Tinubu a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Wike ya tsage gaskiya kan rawar da ya taka wajen soke takarar gwamnan APC a 2027

“Burimmu shi ne mu samu masu zaɓe da magoya baya miliyan 20 a faɗin ƙasar nan domin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a shekarar 2027.” In ji shi.
Ana neman kuri'u ga Tinubu
Mai girma Bola Tinubu a wajen yakin neman zaben APC a Jigawa Hoto: Stanley Kingsley Nkwocha
Source: Facebook

Tinubu ya yi magana kan Atiku

A wani labarin kuma, kun ji cewa Bola Ahmed Tinubu ya yi tambaya kan ƙarfin siyasar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, a jiharsa ta Adamawa.

Tinubu ya yi ikirarin cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasar ba shi da goyon bayan manyan ’yan siyasa da masu ruwa da tsaki a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng