Yadda aka Shigo da Tarin Makamai Najeriya ana Shirin Zaben 2027

Yadda aka Shigo da Tarin Makamai Najeriya ana Shirin Zaben 2027

  • Hukumar tsaro ta DSS ta cafke bindigogi kirar AK-47 guda 21 da manyan bindigogin PKT guda hudu a wani yanki na jihar Sokoto
  • Ta ce an kama makaman ne a Dawakawa da ke karamar hukumar Goronyo, bayan sanya ido kan wasu da ake zargin masu safarar makamai ne
  • Haka kuma, DSS ta kama mata da dama da ake zargin masu kai wa ’yan bindiga makamai ne a jihohin Najeriya daban-daban

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Sakkwato – Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta sanar da cafke wasu makamai da alburusai da aka yi safararsu daga Jamhuriyar Nijar zuwa Najeriya, a wani samame da jami’anta suka gudanar a jihar Sokoto.

An kama makaman ne a Dawakawa, karamar hukumar Goronyo, yayin da ake zargin wasu kungiyoyin ’yan ta’adda na kokarin shigar da makamai kasar domin amfani da su wajen tada zaune tsaye kafin da lokacin babban zaben 2027.

Kara karanta wannan

Pantami ya shiga Gombe duk da kona tayoyi, toshe hanya da kai masa hari

Wasu jami'an DSS
Ma'aikatan huumar tsaro ta DSS. Hoto: Getty Images
Source: Twitter

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa makaman sun hada da bindigogin AK-47 guda 21, manyan bindigogin PKT guda hudu da kuma harsashi 825.

Hanyar safarar makamai

Wata majiya ta tsaro ta bayyana cewa bayan da DSS ta kara kaimi wajen cafke makaman da ake safararsu a sassan Najeriya, wasu kungiyoyin ’yan ta’adda sun koma amfani da mata da dabbobi wajen jigilar makaman.

Majiyar ta ce ana amfani da rakuma musamman wajen safarar makaman ba bisa ka’ida ba, domin kauce wa binciken jami’an tsaro.

Ta kuma bayyana cewa jami’an DSS sun gano wani kwamandan ’yan ta’adda da ake zargin an daura wa alhakin haddasa tashin hankali gabanin zaben 2027 da kuma lokacin gudanar da shi.

An kama mata 14 da ake zargi

A farkon makon nan, jami’an DSS sun kama wata mata mai suna Hafsat Umar a karamar hukumar Talata Mafara ta jihar Zamfara.

An kama ta ne da gurneti guda 12 da bel din alburusai guda biyu. Rahoton ya bayyana cewa ita ce mace ta 14 da DSS ta kama bisa zargin safarar makamai tsakanin watan Fabrairun 2025 da Nuwamban 2026.

Kara karanta wannan

Hukumar Hisbah ta dawo kan mata a jihar Katsina, an kafa dokar hana talla

Bayanan sirri sun nuna cewa Hafsat ta yi tafiya zuwa jihar Neja domin samo alburusai da za ta kai wa wani fitaccen shugaban ’yan bindiga, Saidu Marafa, wanda ke zaune a Kani Kawa, karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara.

The Nation ta wallafa cewa kamen da DSS ta yi wa matan da ake zargin masu safarar makamai ne ya shafi jihohin Zamfara, Nasarawa, Ebonyi, Taraba, Kaduna da Filato.

Makaman da aka kwato a jihohi

Daga cikin matan da DSS ta kama akwai Aisha Mohammed, wadda aka cafke a watan jiya a Keffi, jihar Nasarawa, bisa zargin safarar makamai da alburusai ta hannun wani dillalin makamai kuma mai garkuwa da mutane da ake kira Sani.

A watan Satumban 2026, jami’an DSS sun kama wasu mata biyu, Chika Aguzie da Blessing Nwamba, a wurare daban-daban a jihar Ebonyi bisa zargin taimaka wa kwamandojin kungiyar ESN wajen samar da makamai da abubuwan fashewa.

Rahoton ya ambaci kwamandojin da ake zargi da karbar makaman, ciki har da Chinonso Amobi Okafor, wanda aka fi sani da Temple, da kuma B44, wadanda ake cewa suna jihar Anambra.

Jami'an DSS a bakin aiki
Wasu jami'an hukumar DSS a wajen aiki. Hoto: Zagazola Makama
Source: Twitter

A watan Agustan 2026, DSS ta kama Rabiatu Halidu a kan titin Abacha, karamar hukumar Katu ta jihar Nasarawa, inda aka same ta da alburusai 501 masu girman 7.62mm.

Kara karanta wannan

Bayan rasa iko a majalisar Amurka, Trump ya dauko sabuwar hanyar nakasa Iran

A watan Fabrairun shekarar, jami’an hukumar sun kama Aisha Ibrahim a Tsafe, jihar Zamfara, da alburusai 975.

Haka kuma, a watan Janairu, an kama Sakina Muhammad da Badariyya Abubakar a kan hanyar Wukari zuwa Jalingo ta jihar Taraba.

DSS ta kuma kama wasu mutane a shekarar 2025, ciki har da Rahane Sanusi a karamar hukumar Talata Mafara ta jihar Zamfara.

An kashe shugaban MACBAN

A wani labarin, mun ruwaito cewa rundunar ’yan sandan jihar Taraba ta fara bincike kan kashe shugaban MACBAN, Alhaji Ibrahim Saidu.

Rahotanni sun bayyana cewa an kashe Saidu ne a yammacin ranar Lahadi, bayan wasu ’yan bindiga sun kai hari gidansa da ke Takum.

Rundunar 'yan sanda ta bayyana cewa bayanan farko sun nuna cewa maharan sun isa gidan marigayin ne a kan babur kafin su kai harin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng