Coronavirus ta sake kashe wasu mutane hudu a Saudiyya

Coronavirus ta sake kashe wasu mutane hudu a Saudiyya

- An sake samun karin mutane hudu da suka mutu a kasar Saudiyya sakamakon cutar COVID-19

- Ma’aikatar lafiya ta kasar Saudiyya ta bayyana cewa a yanzu jumullar wadanda suka mutu a kasar ya kai 84

- An samu sabbin mutane 518 da aka tabbatar sun kamu da cutar a kasar, wanda jumullar adadinsu ya kai 6,380

Ma’aikatar lafiya ta kasar Saudiyya ta bayyana cewa, annobar coronavirus ta sake kashe mutane hudu, sun mutu a kasar a cikin sa’o’i 24 da suka gabata.

A yanzu jumullar wadanda suka mutu a kasar ya kai 84.

Mai magana da yawun ma'aikatar, ya bayyana cewa mutane hudun da suka mutu ba 'yan Saudiyya ba ne, kuma suna fama da wasu cutukan na daban, Jaridar Saudi Gazette ta ruwaito.

An kuma tattaro cewa shekarun mamatan ya kama daga 35 zuwa 89.

Coronavirus ta sake kashe wasu mutane hudu a Saudiyya

Coronavirus ta sake kashe wasu mutane hudu a Saudiyya
Source: UGC

Har ila yau, kakakin ma'aikatar ya ce an samu sabbin mutane 518 da aka tabbatar sun kamu da cutar a kasar, wanda jumullar adadinsu ya kai 6,380.

"Daga cikinsu, 990 sun warke bayan samun rahoton 59 da suka warke a cikin sa'a 24 da suka wuce," a cewar ma'aikatar lafiyar.

KU KARANTA KUMA: Sakamakon gwajin mutane 90 da ke nuna alamun COVID-19 a Abuja ya fito, basa dauke da cutar

A wani labarin kuma, mun ji cewa ma’aikatar lamuran addinin Musulunci, Da’awah, da shiryar da a’umma na Saudiyya ta bayyana cewa mutane su shirya gudanar da Sallar Tarawihi a gidajensu saboda ba za'a bude Masallatai ba.

Sallar Tarawihi wacce aka fi sani da Sallar Asham, wasu raka’o’i ne da ake gudanarwa bayan Sallan Isha’i a cikin watar Ramadana.

Gwamnatin Saudiyya ta ce sam ba zata daga dokar rufe Masallatai ba sai cutar Coronavirus ta kare gaba daya.

Jaridar Al-Riyadh ta ruwaito Ministan lamuran addinin Musulunci, Dr. Abdul Latif Al Sheikh, da cewa Sallolin farilla biyar da aka dakatar sun fi Tarawihi muhimmanci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel