Katsina: An fara bi gida - gida neman wadanda suka dawo daga Abuja da Legas

Katsina: An fara bi gida - gida neman wadanda suka dawo daga Abuja da Legas

Gwamnatin jihar Katsina fa fara bi gida - gida neman wadanda su ka shigo jihar daga Legas da Abuja kwanan nan.

Kwamishinan yada labarai a jihar Katsina, Mohammed Serika, ne ya sanar da hakan yayin da ya ke magana da manema labarai ranar Laraba.

Ya bayyana cewa sun yanke shawarar yin hakan ne saboda wasu daga cikin wadanda suka dawo daga Legas da Abuja sun kauracewa cibiyoyin bincike da aka kafa a iyakokin jihar..

"Kwamitin da aka kafa ya na samun hadin kan jama'a, ta hanyar kiransu tare da ba su bayanai a kan mutanen da ake zargi su na dauke da kwayar cutar covid-19.

"Kwamitin zai hada kai da sauran ma su ruwa da tsaki domin gano irin wadannan mutane domin killacesu da gudanar da gwaji a kansu.

"Gwamnati ta dukufa wajen ganin ta gano wadanda su ka yi ma'amala da ma su dauke da kwayar cutar domin killacesu da gudanar da gwaji a kansu.

"Ta hakan ne kawai za a samu nasarar dakile yaduwar annobar a jihar, wacce ta bulla a karamar hukumar Daura a cikin makon jiya," a cewarsa.

Katsina: An fara bi gida - gida neman wadanda suka dawo daga Abuja da Legas
Aminu Masari
Asali: Twitter

An wani labarin na daban, Legit.ng ta wallafa cewa an harbi wani matashi yayin da dandazon mata da matasa su ka fito domin gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewa da tsawaita dokar hana fita a karamar hukumar Sapele da ke jihar Delta.

Matashin da aka harba ya na daga cikin daruruwan fusatattun matasa da mata da su ka fito gudanar da zanga-zangar nema a basu tallafin jin kai tunda aka kara wa'adin sati biyu a kan dokar kulle da hana jama'a fita.

DUBA WANNAN: Rundunar 'yan sanda ta cafke wata mata da ke safarar makamai ga masu garkuwa da mutane

Duk da an samu rudani a kan harbin matashin, majiyar jaridar 'The Nation' ta rawaito cewa daya daga cikin jami'an tsaro da suka zo domin kwantar tarzoma ne ya harbe shi.

Majiyar ta bayyana cewa an garzaya da matashin zuwa wani asibiti domin ceton ransa.

"Jami'an tsaro sun zo wurin domin tarwatsa ma su zanga - zangar. Ina jin a kokarin tarwatsa jama'ar ne su ka harbi matashin a kugu," a cewar majiyar, wacce ta nemi a boye sunanta.

Yayin zanga - zangar, fusattaun matasan sun dinga rera wakar "a bamu abinci, "ba zamu saurari duk wani zance ba".

A ranar Talata ne gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, ya fitar da sanarwar kara sati biyu a kan dokar hana fita daga gida da taron jama'a biyo bayan karewar wa'adin sati biyun farko da ya ayyana.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel