'Yan fashi sun kai wa 'yan sandan kan hanya hari, sun yi awon gaba da AK47 3, sun kone motar sintiri

'Yan fashi sun kai wa 'yan sandan kan hanya hari, sun yi awon gaba da AK47 3, sun kone motar sintiri

Wasu gungun 'yan fashi da makami su 6 sun kai hari a kan shingen kan hanya na jami'an 'yan sanda a Enugu, tare da yin awon gaba da bindigu kirar Ak47.

Tawagar 'yan fashin sun kai harin ne a cikin babur mai kafa uku da aka fi sani da 'keke', inda suka raunata 'yan sanda uku tare da kone musu motar sintiri.

Jaridar Punch ta rawaito cewa lamarin ya faru ne ranar Talata a kan hanyar Enugu zuwa Nsukka a yayin da 'yan sandan suka tsare hanyoyi domin tilasta wa jama'a biyayya ga dokar hana zirga-zirga da walwala saboda annobar covid-19.

Wata majiya a cikin jami'an tsaro ta sanar da Punch cewa 'yan ta'addar, sanye cikin bakaken kaya, sun fara kai harin ne a kan shingen kan hanya da ke Ekwegbe, inda suka raunata wani dan sanda mai suna Insifekta James.

'Yan ta'addar sun kara kai wa wasu 'yan sandan hari a shingen kan hanya na gaba da suka tarar a kan hanyar Enugu zuwa Nasukka, inda suka raunata 'yan sanda guda biyu tare da yin awon gaba da bindigunsu kirar Ak47.

'Yan fashi sun kai 'yan sandan kan hanya hari, sun yi awon gaba da AK47 3, sun kone motar sintiri
'Yan fashi sun kai 'yan sandan kan hanya hari, sun yi awon gaba da AK47 3, sun kone motar sintiri
Asali: UGC

Majiyar ta bayyana cewa 'yan sandan da da aka kaiwa harin su na aiki ne a karkashin tawagar tabbatar da tsaro a manyan hanyoyi SHW (safer highways ways).

A cewar majiyar, an raunata biyu daga cikin 'yan sandan tare da yin awon gaba da bindigunsu, yayin harin da aka kai musu su na bacci.

"Sun raunata 'yan sanda biyu, sun kwashe bindigunsu na aiki, sannan su ka saka wa motar 'yan sandan da ke wurin wuta," a cewar majiyar.

DUBA WANNAN: Sautin murya: Shekau ya yi laushi a cikin sabon sakon da ya fitar don karfafawa mayakansa gwuiwa

Punch ta rawaito cewa wakilinta ya samu sahihin labarin cewa an garzaya da jami'an 'yan sandan zuwa wani asibiti da ba a bayyana sunansa ba, domin a duba lafiyarsu.

Kokarin Punch na jin ta bakin kwamishinan 'yan sandan jihar Enugu, Ahmad Abdur-rahma, ko kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Daniel Ndukwe, bai samu ba.

Amma, babban jami'in dan sanda da ke kula da rundunar SHW a Enugu, SP Sam Agbons, ya tabbatar da labarin kai harin, tare da bayyana cewa babu asarar rai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel