Mele Kyari: Kasuwar danyen mai ta ragu da ganguna miliyan 6 a Maris

Mele Kyari: Kasuwar danyen mai ta ragu da ganguna miliyan 6 a Maris

A halin yanzu Najeriya ta soma ganin tasirin annobar COVID-19 a tattalin arzikinta. Kamfanin man Najeriya watau NNPC, ya ce kasuwar danyen man kasar ya fara raguwa sosai.

Shugaban kamfanin NNPC, Mele Kolo Kyari, ya ke cewa sun gamu da raguwar ciniki a cikin Watan Maris inda aka rasa wanda zai saye gangunan danyen mai miliyan 6.8 a kasuwa.

Kamar yadda rahotanni su ka bayyana, shugaban NNPC ya yi wannan jawabi ne a lokacin da aka yi hira da shi a gidan talabijin Channels TV a jiya Ranar Laraba, 7 ga Watan Afrilu, 2020.

Alhaji Mele Kolo Kyari ya ce ba Najeriya kadai ta ke fama da wannan matsala ba. Kyari ya yi karin haske da cewa an rage neman danyen mai a kasuwar Duniya a dalilin annobar COVID-19.

Da aka tambayi Mele Kyari a shirin Sunrise Daily da ake yi a lokacin hantsi, shugaban kamfanin na NNPC ya nuna cewa abubuwa su na yin sauki bayan karyewar farashi kwanakin baya.

“Abubuwa sun jagwalgwale a kasuwa, amma yanzu ana samun sauki. A makon jiya mai ya kai kusan $15 a kowane ganga, amma yanzu da na ke magana haka, ganga ta kai $32.79.”

KU KARANTA: Babu maganar aure ko saki a Dubai sai an ga bayan Coronavirus

Mele Kyari: Kasuwar danyen mai ya ragu da ganguna miliyan 6.8 a Maris

Shugaban Kamfanin NNPC ya ce danyen man Najeriya ya gamu da raguwar ciniki a kasuwa
Source: UGC

Kyari ya ce: “Mu na tunanin a yadda abubuwa su ke wakana, kasashe su na komawa bakin aiki kamar yadda ake gani Turai, za a koma rububin mai a Duniya, ciniki zai karu a kasuwa.”

A cewar Mele Kyari: “A Watan Maris kawai mun rasa kusan ganguna miliyan 6.8. Idan abubuwa su ka dawowa daidai, za mu murmure, mu tabbata kasuwa ta girgije ta dawo daidai.”

Alhaji Kyari ya ke cewa tattaunawa ta yi nisa tsakaninsu da kungiyar OPEC ta kasashe masu arzikin mai da sauran masu hako mai da ‘yan kasuwa donin ganin farashi ya mike.

A karshe Kyari ya nuna cewa ana sa ran kafin karshen wannan shekara, farashin gangar danyen man ya tashi sama a kasuwa. Karyewar farashin ya taba kasafin kudin Najeriya na 2020.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel