Gwamna Zulum ya rufe gidaje mai 10 a Borno

Gwamna Zulum ya rufe gidaje mai 10 a Borno

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya janye takardar mallakar fili na wucin gadi na wasu gidajen sayar da man fetur guda 10 da ke Maiduguri bayan samunsu da laifin boye man fetur.

A cikin wani jawabin da sakataren gwamnatin jihar, Usman Jidda, ya fitar a Maiduguri, ya ce gwamna Zulum ya kwace lasisin gidajen man ne bisa ikon da doka ta bashi a kundin tsarin dokokin mallakar filaye.

"Mai girma gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayar da umarnin janye takardun mallaka tare da fara daukan matakan kwace filayen wasu gidajen man fetur 10 bisa tanadin dokokin mallakar filaye da ikon da doka ta bashi.

"Gwamnati tana gargadin sauran gidajen mai da su guji yin duk wani abu da kan iya zama cin dunduniya ga tattalin arzikin jihar Borno, kuma gwamnati za ta cigaba da sa ido a kan harkokin gidajen sayar da man fetur da ke fadin jiha.

"Gwamnati ba za ta yi shakkar daukan matakan da doka ta amince da su ba domin hukunta gidajen man da aka samu da irin wannan hali," a cewar sanarwar.

Gwamna Zulum ya rufe gidaje mai 10 a Borno

Farfesa Babagana Zulum
Source: Facebook

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa wasu gidajen sayar da man fetur a jihar Borno sun boye mai tare da sayar da shi a farashi mai tsada tun bayan sanarwar matakan dakile yaduwar annobar cutar covid-19.

Hakan ne yasa gwamna Zulum da kansa ya kai wata ziyarar bazata a irin gidajen man da ake zargi da aikata hakan domin tilasta su budewa tare da sayarwa da jama'a man a kan farashin da gwamnati ta yanke.

DUBA WANNAN: SGF ya mayar da martani a kan jita-jitar Buhari ya sallami Abba Kyari

A wani labarin da ya shafi jihar Borno, Legit.ng ta wallafa cewa jiragen yaki na rundunar sojin sama ta Najeriya, a karkashin atisayen 'Operation Lafiya Dole', sun yi luguden wuta tare da baje daya daga cikin manyan mafakar mayakan kungiyar Boko Haram da ke Parisu a cikin dajin Sambisa.

Luguden wutar ya yi sanadiyyar mutuwar dumbin mayakan kungiyar Boko Haram tare da lalata dukkan sansanin.

A cikin jawabin da darektan yada labaran atisayen rundunar soji, Birgediya Janar Benard Onyeuko, ya fitar, ya ce rundunar soji za ta cigaba da rike wuta a yakin da take yi da 'yan ta'adda.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel