Yanzun-nan: Coronavirus ta kashe mutum na farko a Saudiyya

Yanzun-nan: Coronavirus ta kashe mutum na farko a Saudiyya

- Saudiyya ta tabbatar da mutuwar mutum na farko a kasar sakamakon cutar coronavirus

- Mutumin da cutar ta kashe ya kasance dan asalin kasar Afghanistan

- An samu karin masu dauke da cutar a kasar da mutum 205 inda yawansu a halin yanzu ya kai 767

Rahotanni daga kasar Saudiyya ta tabbatar da mutuwar mutum na farko a kasar sakamakon cutar coronavirus.

Ma'aikatar lafiya ta kasar ta bayyana cewa wanda cutar ta kashe dan asalin kasar Afghanistan ne kuma mai shekaru 51, shafin BBC Hausa ta ruwaito.

Saudiyya ita ce kasar da ta fi yawan masu cutar a Gabas ta Tsakiya bayan Iran.

Yanzun-nan: Coronavirus ta kashe mutum na farko a Saudiyya
Yanzun-nan: Coronavirus ta kashe mutum na farko a Saudiyya
Asali: Facebook

A ranar Talata, 24 ga watan Maris, an samu karin masu dauke da cutar da mutum 205 inda yawansu a halin yanzu ya kai 767.

KU KARANTA KUMA: Za ayi bincike game da ingancin takardar umarnin Abba Kyari – Majalisar Wakilai

A baya mun ji cewa mai alfarma Sarkin Saudiyya, Sarki Salman bin Abdulaziz ya sanya dokar hana shige da fice a kafatanin kasar Saudiyya daga karfe 7 na dare zuwa 6 na safiyar kowanne rana na tsawon kwanaki 21 don rage yaduwar cutar Coronavirus.

Jaridar Alarabiya ce ta ruwaito kamfanin dillancin labaru na kasar Saudiyya ta fitar da sanarwar, wanda tace umarnin Sarkin zai fara aiki ne daga ranar Litinin, 23 ga watan Maris na shekarar 2020.

Sanarwar ta kara da cewa ma’aikatan kula da al’amuran cikin gida ce za ta tabbatar da dabbaka dokar tare da hadin kan hukumomin Soji, Yansanda da sauran hukumomin farin kaya da aikin tabbatar da bin doka ya shafa.

Gwamnatin ta nemi jama’a su zauna a gidajensu a lokacin dokar, kada wanda ya fito har sai ta kama, kamar domin duba lafiyarsu. Sai dai dokar ta daga kafa ga muhimman ma’aikatan gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu.

Daga cikin wadanda dokar ta daga ma kafa akwai jami’an tsaro, Sojoji, yan jaridu, ma’aikatan kiwon lafiya, jami’an ma’aikatun kudi, jami’an kamfanonin sadarwa da kuma jami’an hukuara ruwan sha ta kasar.

Gwamnatin ta dauki wannan mataki ne sakamakon samun hauhawar masu kamuwa da cutar a Coronavirus a kasar Saudiyya, inda a yanzu adadinsu ya kai mutum 511, kamar yadda kaakkain ma’aikatan kiwon lafiya na kasar, Mohamemd Al-Abd al-Ali ya bayyana.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel