Iyalin El-Rufai sun fi morewa a lokacin da bai zama Gwamna ba – Inji Aisha Ummi
A matsayinta na daya daga cikin Matan mai girma gwamna, Aisha Ummi Garba El-Rufai, ta yi karin haske game da halin da su ke ciki duk da matsayin da Mai gidansu ya ke rike da shi.
Hajiya Aisha Ummi Garba El-Rufai ta yi hira ne da ‘Yar jarida Vimbai Mutinhiri kwanakin baya, inda ta fayyace abin da jama’a ba su sani ba game da Iyalin gwamnan na jihar Kaduna.
Ummi Garba El-Rufai ta nuna cewa kuskuren da jama’a su ke yi shi ne yi wa Mai dakin gwamna kallon mai kudi, ta ce kowa ya na tunanin Matar gwamna a Najeriya ta na da tarin dukiya.
Mai dakin gwamnan ta ce: “Mun fi jin dadin rayuwarmu kafin Mijina ya zama Shugaba. Ta fuskar arziki, sosai, saboda ya na maida rabin albashinsa na wata cikin dukiyar gwamnati.”
“Dole kuma mu takawa kanmu burki wajen harkar dukiya daga facaka domin gudun jama’a su rika yi mana kallon mu na daukar kudi daga asusun gwamnati.” Inji Ummi El-Rufai.
Matar gwamnan na jam’iyyar APC ta ce ba zai dace mutane su rika tunanin Iyalin El-Rufai su na barna da dukiya fiye da yadda su ka saba kafin zaman Mai gidan na su gwamna a 2015.
KU KARANTA: Shugabannin Najeriya sun mallaki tulin dukiya a Dubai - Bincike
Wani abu da ke ci wa Hajiya Ummi Garba El-Rufai tuwo a kwarya shi ne irin bukatan da ‘Yanuwa ko Abokai su ke kawowa gaban Iyalan gwamna ganin cewa su ke rike da tulin kudin jihar.
“Ina ganin wannan shi ne babban kuskuren da ake yi a kan Matan shugabanni. Haka ‘Yanuwa sai su dauka ku na da makudan kudi ne, su rika kawo wasu mahaukatan bukatu gabanku.”
“Idan har ka ce ba ka da wadannan kudi, sai a fara kukan cewa ya za ayi ace su na kan mulki, amma ba za ta taimaka ba. Jama’a su na yi maka kallon inda ba ka kai ba” Inji Ummi.
Wani abu da ba a sani ba shi ne, Matar gwamna ba za ta iya juya Jami’an gwamnati ba. “Ina auren Gwamna, amma ba za ka zo wurina ka ce in fadawa Kwamishina ya yi maka wani abu ba.”
A cewar Matar gwamnan, ba ta da karfin ikon da za ta umarci Kwamishinan Mai gidanta da ya yi wa mutum wata alfarma, ta ce har ta saba da cewa jama’a a’a ba tare da ta ji ta yi laifi ba.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng