Wasika zuwa ga ‘Dana: Sanusi Lamido Sanusi - Baba Ahmed Joda

Wasika zuwa ga ‘Dana: Sanusi Lamido Sanusi - Baba Ahmed Joda

Tsohon Sakataren din-din-din na gwamnatin tarayya, Ahmed Joda, ya shiga cikin sahun wadanda su ka yi magana game da tsige Muhammadu Sanusi daga sarauta.

Alhaji Ahmed Joda ya rubuta wata budaddiyar wasika a Jaridar Daily Trust ga tsohon Sarkin Birnin Kano watau Malam Muhammadu Sanusi II wanda ya kira da Yaronsa.

A wannan wasika, Ahmed Joda ya nuna cewa a halin yanzu bai san inda tsohon Sarkin ya ke zama ba, a sakamakon tunbukesa da gwamnatin jihar Kano ta yi daga kan mulki.

Joda mai shekaru 90 a Duniya ya nuna cewa ya san Malam Sanusi II tun ya na 'Dan karamin yaro mai shirin shiga makarantar sakandare, a wancan lokaci ya na kiransa ‘Baba.’

Haka zalika Joda ya bayyana cewa ya san Kakakansa Muhammadu Sanusi II, haka zalika ya shaku sosai da Mahaifinsa, Aminu Sanusi da ‘Danuwansa Marigayi Ado Sanusi.

A wasikar ta sa, Joda wanda tsohon Sarkin ya ke kira Baba Joda ya bayyana Iyayen Sanusi II a matsayin mutane masu hangen nesa da mutunci da tunani da tsayin-daka.

KU KARANTA: Sanusi II ya kai Shugaban 'Yan Sanda da Darektan DSS kotu

Wasika zuwa ga ‘Dana: Sanusi Lamido Sanusi - Baba Ahmed Joda
Ahmed Joda ya rubuta wasika ga Sanusi Lamido Sanusi da aka tunbuke
Asali: Instagram

A lokacin da ya fara haduwa da Sanusi II a lokacin ya na yaro, Dattijon ya ce ya gane cewa Ubangiji ya tara masa basira, wanda a karshe Duniya ta tabbatar da hakan.

Tun farko, Joda ya ce ya hango barin Sanusi II kan gadon mulki, amma ya bayyana cewa wannan rashi zai iya zama wani alheri ga al’ummar Kano da daukacin kasar Najeriya.

Tsohon ma’aikacin gwamnatin ya yi kira ga Sanusi II da cewa ya cigaba da abin da aka san shi da shi, sannan kuma ya roke shi da ya bada gudumuwa wajen kawo gyara a al’umma.

A takardar, Joda ya tabbatar da cewa tsohon Sarkin mutum ne mai ilmin zamani na boko da na addinin Musulunci. Duniya dai ta shaida irin dinbin ilmin Malam Sanusi II.

A dalilin wannan baiwa da Sanusi II ya ke da ita, Ahmed Joda ya ce ya san zai yi hakuri da halin da ya samu kansa a wannan lokaci, ya kuma bukaci ya kawowa kasar dauki.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel