Sanusi na rayuwa tamkar dan fursuna yayin da yan sanda da NSCDC suka hana baki ganinsa - Rahoto

Sanusi na rayuwa tamkar dan fursuna yayin da yan sanda da NSCDC suka hana baki ganinsa - Rahoto

Rahotanni sun kawo cewa Muhammadu Sanusi II, tsohon sarkin Kano da aka tsige, na nan yana rayuwa tamkar dan gidan yari tun bayan da aka kais hi karamar hukumar Awe da ke jahar Nasarawa.

A cewar mazauna yankin, an hana wasu mutane da suka kai ziyara ganin Sanusi wanda aka dauke daga Kano a yammacin ranar Litinin, jaridar The Cable ta ruwaito.

An rahoto cewa akalla jami’an yan sanda da na NSCDC 30 ne ke gadin sabon muhallin tsohon gwamnan na babban bankin Najeriya (CBN).

Kimanin yan sanda uku zuwa biyar ne ke tsaye a kofar shiga gidan, inda suke hana mutane shiga baya ga yan tsirarun mutane daga cikin iyalan tsohon sarki da kuma jami’an gwamnati da ke shiga ciki don ganin Sanusi.

Sanusi na rayuwa tamkar dan fursuna yayin da yan sanda da NSCDC suka hana baki ganinsa - Rahoto

Sanusi na rayuwa tamkar dan fursuna yayin da yan sanda da NSCDC suka hana baki ganinsa - Rahoto
Source: UGC

Sauran yan sandan kuma na tsaye a sako daban-daban don kula da yadda mutane da ba a sani ba ke daukar hotuna da bidiyon gidan da kuma abokan aikinsu.

A lokacin sallah, jami’in dan sanda daya ko biyu ne ke gadin kofar, yayinda sauran ke zuwa yin sallah a masallacin da ke kusa.

An kuma rahoto cewa jami’an tsaro sun sanar da manema labarai da suka nemi izinin shiga gidan a lokuta daban-daban cewa an umurce su da kada su bar kowa ya shiga.

Wani jami’in dan sanda rike da bindigar AK-47 ya ce: “duk nisan inda kuka fito kuka zo nan, na tabbata abokan aikina ba za su bari ku shiga ciki ba."

KU KARANTA KUMA: Tsige Sanusi II: Farfesa Auwal Yadudu da Sanata Shehu Sani sun yi magana

Yan sanda sun kama daya daga cikin magoya bayan Sanusi wanda aka hana shiga ciki amma ya yi kokarin daukar hotunan gidan, inda suka kwace wayoyinsa sannan suka bukaci da ya rike kunnuwansa sannan ya yi tsallan kwado.

A wani labarin kuma mun ji cewa Mista Peter Obi wanda tsohon gwamnan jihar Anambra ne, ya yi Allah-wadai da tsige Muhammadu Sanusi II da aka yi daga kan sarautar kasar Kano.

Peter Obi wanda ya yi takarar mataimakin shugaban kasa a 2019 ya bayyana cewa illar tsige Sarkin yi ta fi tasiri a kan Najeriya a kan shi Muhammadu Sanusi II.

A na sa ra’ayin, tunbuke Malam Muhammadu Sanusi II ya jawowa Najeriya mummunan hadari fiye da illar da ya kamata a ce tsigewar ta yi wa tsohon Sarkin na Kano.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel