Yanzun nan: Sanatoci sun nemi Buhari ya tsige shugabannin tsaron kasar

Yanzun nan: Sanatoci sun nemi Buhari ya tsige shugabannin tsaron kasar

- Gamayar wasu sanatoci sun bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya sallami shugabannin tsaron kasar

- Wadanda suka yi wannan kira sun hada da Shugaban marasa rinjaye a Majalisar dattawa, Sanata Enyinnaya Abaribe, sanata Musa Sani, Betty Apiafi da Solomon Adeola

- A cewar yan majalisar, ya kamata a sauya shugabannin tsaron tunda basu da sabbin dabarun yaki da rashin tsaro a kasar

Wasu sanatoci sun bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya sallami shugabannin tsaro na kasar.

Sun kuma yi kira ga murabus din sufeto janar na yansanda, Mohammed Adamu.

Yan majalisar sun gabatar da bukatar ne a gudunmawarsu kan tattaunawa da aka yi game da lamarin tsaro a kasar a lokacin zaman majalisa a ranar Laraba, 29 ga watan Janairu.

Wadanda suka yi wannan kira sun hada da Shugaban marasa rinjaye a Majalisar dattawa, Sanata Enyinnaya Abaribe, sanata Musa Sani, Betty Apiafi da Solomon Adeola.

Yayinda sanata Sani ya yi kira ga murabus din Shugaban yan sanda, Apiafi da Adeola sun bukaci shugaban kasar da ya tsige dukkanin shugabannin tsaro.

Yanzun nan: Sanatoci sun nemi Buhari ya tsige shugabannin tsaron kasar
Yanzun nan: Sanatoci sun nemi Buhari ya tsige shugabannin tsaron kasar
Asali: UGC

A cewar yan majalisar, ya kamata a sauya shugabannin tsaron tunda basu da sabbin dabarun yaki da rashin tsaro a kasar.

Shugabannin tsaron sun hada da shugaban ma’aikatan tsaro, Janar Abayomi Olonisakin; Shugaban rundunar soji, Laftanal Janar Tukur Buratai; Shugaban sojin sana, Air Marshal Sadique Abubakar da kuma shugaban sojin ruwa, Ibok Ekwe Ibas.

KU KARANTA KUMA: An rantsar da Doguwa a matsayin shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa, Sanata Eyinnaya Abaribe, ya yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari yayi murabus kan gazawar gwamnatinsa wajen magance matsalolin tsaron da suka addabi Najeriya.

Abaribe ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a zauren majalisa yayinda ake tafka muhawara kan rashin tsaro a kasar.

Yace: "Mun yan Najeriya ba IGO muka zaba ba, ba hafsoshin Soji muka zaba ba. Gwamnatin APC muka zaba a 2015. Muna kira ga wannan gwamnatin tayi murabus saboda ta gaza wanzar da hakkinta."

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel