Yanzun nan: Zabukan gwamna: An janye Shugaban alkalan Najeriya daga kwamitin kotun koli

Yanzun nan: Zabukan gwamna: An janye Shugaban alkalan Najeriya daga kwamitin kotun koli

- Shugaban alkalan Najeriya, Justis Tanko Muhammed bai halarci zama ba a lokacin da kotun koli ta fara yanke hukuncinta kan zaben gwamnan jihar Kano

- Justis Sylvester Ngwuta ke jagorantar kwamitin alkalan mai dauke da mambobi biyar a madadin Tanko

- A halin yanzu, Kotun Kolin Najeriya ta yi watsi karar Abba Kabir Yusuf, ta tabbatar da Dakta Abdullahi Umar Ganduje matsayin zababben gwamnan jihar Kano a zaben Maris, 2019

Shugaban alkalan Najeriya, Justis Tanko Muhammed bai halarci zama ba a lokacin da kotun koli ta fara yanke hukuncinta kan karar da aka daukaka kan zaben gwamnan jihar Kano.

A madadinsa, Justis Sylvester Ngwuta ke jagorantar kwamitin alkalan mai dauke da mambobi biyar.

Sauran sun hada dan Justis Kudirat Kekekere-Ekun, Justis Olukayode Ariwoola, Justis Amina Augie da kuma Justis Uwani Abba-Aji.

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Kotun Kolin Najeriya ta yi watsi karar Abba Kabir Yusuf, ta tabbatar da Dakta Abdullahi Umar Ganduje matsayin zababben gwamnan jihar Kano a zaben Maris, 2019.

Alkalan kotun gaba daya karkashin jagorancin Jastis Sylvester Ngwuta sun yi ittifakin cewa karar da Abba Kabir Yusuf ya shigar bata da karfi.

KU KARANTA KUMA: Jama’a na tserewa yayinda Boko Haram suka karbe hanyar Damaturu-Maiduguri

Dan takarar Peoples Democratic Party (PDP), Abba Kabir Yusuf, ya shigar da kara ne kan karashen zaben Kanon da akayi ranar 23 ga watan Maris bayan shi ke kan gaba a zaben da akayi ranar 9 ga Maris.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel