Kotu ta ba EFCC izinin tsare Shehu Sani na tsawon kwanaki 14
Hukumar EFCC ta samu yardar kotu na tsare Sanata Shehu Sani har tsawon kwanaki 14 domin bayar da damar bincike kan zarginsa da hannu a badakalar wasu kudade.
Lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban kamfanin motar ASD, Alhaji Sani Dauda, ya yi watsi da ikirarin Shehu Sani, inda yace lallai yana kan bakarsa kan korafin da ake kan sanatan.
Korafin ya kuma yi zargin cewa Shehu Sani ya ajiye sunan shugaban alkalan Najeriya, inda ya bukaci ya biya naira miliyan 4 wanda shi shugaban alkalan zai raba ma alkalai 4 da za su tabbatar da ganin cewar karar da wani Abubakar ya shigar kan shugaban na ASD bai cimma nasara ba.
Korafin ya kuma yi zargin cewa sanatan ya bukaci naira miliyan 1 ga jami’an EFCC.
Ya kara da cewa ya biya naira miliyan 5 a dala ga alkalan hudu da jami’an EFCC ta hannun Shehu Sani.
Ya kuma yi ikirarin cewa sanatan ya dawo a ranar 29 ga watan Nuwamba, 2019, cewa mai kara kan shari'arsa ba zai iya yin komai ba amma ya yi magana da Magu ya ce ya kawo $20,000 don magance lamarin.
Ya yi zargin cewa ya shiga juyayi ganin cewa Magu baya rashawa. Amma Sanatan ya yi zargin cewa Magu abokinsa ne sannan cewa zai karbi cin hanci.
Mai karar ya ci gaba da cewa ya ba Shehu Sani $10,000 a ranar 29 ga watan Nuwamba, 2019.
Ya kuma yi zargin cewa tun aga lokacin Shehu Sani ya daina daukar wayarsa sannan ya yi buris da sakonninsa.
KU KARANTA KUMA: A karshe: Wanda ya kitsa fashin bankin Abuja ya shiga hannu
A baya mun ji cewa hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta damke Shehu Sani, Sanatan da ya wakilci mazabar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa tsakanin 2015 da 2019. The Nation ta ruwaito.
A cewar majiyar, an damke Shehu Sani ne kan zargin karban $20,000 daga hannun mai kamfanin motocin ASD. Majiyar tace: "An ce ya karbi $20,000 daga hannun mai kamfanin ASD da sunan cewa shi abokin shugaban EFCC."
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng