APC bata taba tunanin tsayar da Buhari a karo na uku ba – Gwamnan Nasarawa

APC bata taba tunanin tsayar da Buhari a karo na uku ba – Gwamnan Nasarawa

Gwamnan jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule ya bayyana cewa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) bata taba tunanin gabatar da shawarar sake tsayawa a karo na uku ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ba gabannin zaben shugaban kasa na 2023.

Gwamnan wanda ya bayyana a shirin Channels TV na ‘Politics Today’ ya bayyana cewa a iya saninsa ba a taba wannan tunanin ba, duba ga irin fahimtar da jam’iyyar ta yiwa shugaba Buhari.

Ya Kara da cewa akwai wasu mutane da suka fahimci cewa duba ga yadda yake mutunta doka, shugaba Buhari ba zai fara kunbiya-kunbiya da kuma sauya kundin tsarin mulki ba don kawai ya cigaba da kasancewa a mulki.

Injiniya Sule ya yi watsi da hasashen cewa ana shirya wannan labari a jam’iyyar, inda yace koda ace hakan ya faru ba zai taba samun karbuwa ba.

“Bana tunanin APC ta taba tunanin ajanda ta uku koda tayi, toh bana daga cikin wannan lamari saboda mutumin da ake magana a kai ba zai taba amincewa dashi ba.

KU KARANTA KUMA: Ban damfari ASD $20,000 ba - Shehu Sani ya bayyanawa EFCC

“Don haka bana tunanin akwai wani da zai dauki irin wannan labari sannan ya tunkari Shugaban kasar game da ajandar shugabanci a karo na uku, domin bana tunanin irin wannan labarin zai karbu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel