Jonathan ya nemi Jami’an tsaro su tsare ran Bayin Allah a Najeriya

Jonathan ya nemi Jami’an tsaro su tsare ran Bayin Allah a Najeriya

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan ya yi kira ga Soji su dage wajen ganin an daina kai wa mutane hare-haren da babu gaira babu dalili.

Dr. Goodluck Jonathan ya yi wannan kira ne a lokacin da wasu Dakarun sojojin ruwa su ka kai masa ziyara a sakamakon harin da aka kai masa.

Kwanakin baya ne aka samu wasu Miyagu sun kai hari gidan tsohon shugaban kasar da ke Otuoke a karamar hukumar Ogbia da ke jihar Bayelsa.

Dakarun Rundunar sojojin ruwan da Jami’an Tawagar Operation Delta Safe sun kai wa Jonathan ziyara ne domin duba yanayin ta’adin da aka yi masa.

Sojojin sun tabbatar da cewa harin da aka kai wa shugaban a Ranar jaji-birin Kirismeti wanda ya ci ran wani Soja, shi ne ya sa su ka zo gidan na sa.

KU KARANTA: Abin da ya jawo motar yakin Soji ta babbake a Jihar Yobe

Kamar yadda mu ka samu labari, Sojojin sun bayyana cewa akwai bukatar a duba abin da ya faru domin ganin irin wannan bai sake faruwa nan gaba ba.

Dr. Jonathan ya nemi Sojojin su rika kokarin bin kwa-kwaf da diddiki wajen bincikensu.

“Ku bi diddiki yayin da ku ke kokarin gano wadanda su ka yi wannan aiki a hukuntasu, kuma ku yi kokari wajen ganin ba a sake yin irin wannan ba.”

Goodluck Jonathan wanda ya bar mulki a 2015, ya fadawa Dakarun su dage wajen ganin ba a sake kai irin wannan hari a ko ina a fadin Najeriya ba.

Manyan jami’an Sojil Akinjide Akinrinade, Saidu Garba, Saidu Garba su na cikin wadanda su ka taka zuwa gidan tsohon Shugaban na Najeriya jiya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel