El-Rufai ya tanadi fushin Ubangiji idan ya rusa cocin Zariya – Abiodun Ogunyemi

El-Rufai ya tanadi fushin Ubangiji idan ya rusa cocin Zariya – Abiodun Ogunyemi

Babban Limamin Darikar Angilikan na Mabiya addinin Kirista da ke Garin Zariya, Abiodun Ogunyemi, ya sake yin magana game da Mai girma gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.

Shehin Malamin Kiristan ya sake bayyana cewa babu yadda za ayi Malam Nasir El-Rufai ya zama shugaban kasa a Najeriya. A cewar Malamin Ubangiji ne ya nuna masa wannan ba kowa ba.

Da ‘Yan jarida su ka tambayi Rabaren Abiodun Ogunyemi, a kan abin da ya sa ya ke bada tabbacin El-Rufai ba zai yi mulki ba sai ya ce: “Ba daga ni bane, na ba ku misalai, kuma su na nan da yawa."

“Mutane kan dura a kai na a kan irin haka. Ba na damuwa. Lokacin da, na fito na ce Goodluck Jonathan ne matsalar Najeriya kuma ba zai kai labari ba. Ba ni ba ne, Ubangiji ne ya fada mani.”

Don haka wannan Malami ya ja hankalin Nasir El-Rufai ya hakura da batun neman shugaban kasa. Ogunyemi ya ce ya taba fadawa Mabiyansa Abiola ba zai yi mulki ba, kuma haka aka yi.

KU KARANTA: Ganduje ya karrama Shugaban Kadiriyya da wani aiki da ya yi

Ya ce: “Idan aka nada ka Bishof, ofishinsa na dauke da aikin Malanta da kuma karamomi. Ban san sauran Limamai ba, amma ni tun da na zama Bishof, Ubangiji ya kan kunsa mani magana.”

Faston ya na kuka ne a kan wani tsohon coci da ya haura shekaru 110 a Zariya da gwamnatin Kaduna ta ke shirin ruguzawa kadarorinsa. "Shi ne coci na biyu da ya fi tsufa a yankin Arewa."

“Ya ce ba zai rusa cocin ba, amma zai taba filin cocin. Shi ya sa na fito na yi magana. Gwamna bai da damar taba dukiyarmu. Zai iya zuwa Garin Kaduna ya taba babban Masallacin Musulmi?”

Babban Faston ya ce an gama magana kan takardun filin cocin tun zamani gwamnatin baya. “Kashim Ibrahim ya fara ba mu takardun fili. Ya saurari fushin Allah idan ya taba cocin.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel