Bafarawa da Wammako sun yi cacar baki a filin jirgin sama a Garin Sokoto

Bafarawa da Wammako sun yi cacar baki a filin jirgin sama a Garin Sokoto

Mun samu labari cewa tsofaffin gwamnonin jihar Sokoto biyu, Attahiru Dalhatu Bafarawa da Aliyu Magatakarda Wamakko sun kaure da wani gajeren rikici a filin jirgin Sultan Abubakar III.

Kamar yadda labari ya zo mana daga bakin wani Hadimin tsohon gwamna, Attahiru Dalhatu Bafarawa, Aliyu Magatakarda Wamakko ya rasa ta cewa a lokacin da Mai gidansa ya rutsa shi.

Mai taimakawa tsohon ‘dan takarar shugaban kasar, Nura Aminu Dalhatu, ya bayyana yadda ta wakana tsakanin ‘yan siyasar a filin hjirgin saman Sokoto a Ranar 9 ga Watan Disamban 2019.

Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya yi wa Attahiru Dalhatu Bafarawa Mataimakin gwamna na kusan tsawon shekaru takwas, amma daga baya ya sauka saboda tsoron majalisa ta tsige shi.

Tsohon gwamna Wammako ya yi wasu kalamai da su ka batawa Dalhatu Bafarawa rai kwanaki. Bayan haduwarsu, ‘Dan siyasar hamayyar ya maidawa Sanatan na APC martani a bainar jama’a.

KU KARANTA: Buhari ya tafi kasar Misra tare da wasu Gwamnonin Najeriya

“Ka ce ni 'Dan ci-rani ne, meyasa ka ke gaida ni yanzu? Na san Ubana da Kakana a nan aka haife su, su ka rayu, su ka mutu. Zan iya kai ka har kabarinsu. Za ka iya kai ni kabarin Kakanka?”

Bayan Bafarawa ya yi wa tsohon Mataimakin na sa wannan tambaya, sai ya yi gum bai ba ce komai ba. A wani kaulin an ce Wammako ya sake nanata cewa Bafarawa ‘dan cirani ne a Gari.

Bayan wannan ‘yan takaddama, ‘yan siyasar sun hau jirgi guda sun kama hanya zuwa babban birnin tarayya Abuja. Aliyu Wammako shi ne Sanata mai wakiltar Arewacin Sokoto a Majalisa.

Aliyu Magatakarda Wamakko ya doke ‘Dan takarar da Mai gidansa ya tsaida a zaben 2007 watau Alhaji Muhammadu Maigari Dingyadi. Tun daga nan ake ta ‘yar tsama har zuwa wannan lokaci.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel