Nesa ta zo kusa: Garin da a ke aure da N50,000 kacal

Nesa ta zo kusa: Garin da a ke aure da N50,000 kacal

Dagacin garin Kera da ke karamar hukumar Garko ta jihar Kano, ya saka dokar kayyade kudin aure da sadaki a garin. Kamar yadda dagacin ya sanar, budurwa kudin aurenta da sadaki su tsaya a N137,000 inda bazawara kuma a dinga biyan N50,000.

Kusan watanni uku kenan da dagacin, dattijon arziki, Malam Bello Musa ya kafa wannan dokar. Amma sai dai iyaye sun nuna tsananin damuwarsu tare da kokawa kan wannan sabon cigaban.

A tattaunawar da gidan rediyon Freedom na Kano yayi da wasu iyayen yara a garin, sun nuna ko kadan ba zasu lamunci wannan sabon tsarin ba. A don haka ne suka shiryA tsaf don kai kokensu gaban hukumar karbar korafe-korafe ta jihar Kano.

DUBA WANNAN: Yadda dalibin jami'ar Legas ya harbi wani mutum a mazakuta

Hakazalika, gidan rediyon Freedom da ke Kano bai yi kasa a guiwa ba wajen tuntubar dagacin garin Kera. Ya kuwa bayyana musu cewa, wannan doka fa sun yanketa ne domin samun maslaha a garin, kuma al'umma da malaman garin duka sun aminta da wannan sabuwar dokar.

kamar yadda gidan rediyon Freedom din ya ruwaito, a watan Janairu na shekarar 2017, mahukunta da masu ruwa da tsaki a akaramar hukumar Danbatta da ke jihar Kano, sun kaddamar da dokar kayyade dukiyar aure, sai dai hakan bata yi tasiri ba don ta samu cikas daga karshe.

Idan aka yi maganar aure a arewa, samari na yawan kokawa akan burin da iyayen yara ke sawa akan 'ya'yansu mata idan aka fara maganar aure. Akan takura samarin da bani-bani wanda hakan ke sanya wa su gwammace gara su zauna hakan babu aure.

A bangaren iyayen 'yan matan kuwa, suna kokawa akan kudaden da suke kashewa ne wajen yin kayan daki da gara. hakan kuwa yasa wasu kan yi dabarar tatsa daga jikin mijin kafin auren don samun a fita kunya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel