Mun shiga fargaba don tsoron rushewar Kannywood - Falalu Dorayi

Mun shiga fargaba don tsoron rushewar Kannywood - Falalu Dorayi

Shakka babu masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood na kan ganiyar fuskantar matsaloli, wanda masu sharhi kan lamura ke ganin tana gab da rushewa.

Daga cikin matsalolin da masana’antar ke fuskanta sun hada da; satar fasaha da rashin zuba jari daga masu wadata da kuma rashin kulawar gwamnati, duk kuwa da cewa ta shafe gomman shekaru da kafuwa.

Babban mai bayar da umurni kuma fitaccen jarumi, Falalu Dorayi ya gaskata wannan hasashe na mutane a hira da ya yi da shafin BBC.

Falalu ya ce a halin da masana'antar ke ciki a yanzu, ya haifar da karayar arziki da durkushewar jari da kuma rufe wasu manyan kamfanonin shirya fina-finai.

Ya kara da cewa tun farkon kafa masana'antar sun dogara ne a kan sayar da fina-finansu ta hanyar CD, "amma da yake yanzu an samu ci gaban fasaha sosai mutane kusan sun daina kallon fim a CD sai a wayoyin hannunsu da sauran sabbin hanyoyi," in ji shi.

Sai dai kuma Falalu na ganin idan dai ba a tashi tsaye ba to lallai wannan na iya zamowa silar rushewar wannan masana'anta da dubban mutane ke cin abinci a cikinta.

KU KARANTA KUMA: Toh fah: CBN na yunkurin dawo da bashin N36bn daga manoma a arewa maso gabas

Ya ce: "Sai dai kawai yawan mutanen da ke cikinta da yawan fadada tunani da ake yi to zai iya taimakawa a farfado da ita.

"Gaskiya akwai faduwar gaba don kuwa inda abincinka yake a ce yau yana tangal-tangal ai dole ciki ya duri ruwa.

"Fatanmu yanzu gwamnati ta shigo cikin lamarin, sannan masu kudi su zo su zuba jari su bude sinimu da yawa a yankinmu. Don kuwa masu harkar sinima sun ma fi masu shirya fina-finan samun kudi.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel