Yanzu Yanzu: Buhari ya shiga labule da gwamnan CBN a fadar shugaban kasa

Yanzu Yanzu: Buhari ya shiga labule da gwamnan CBN a fadar shugaban kasa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin, 28 ga watan Oktoba, ya yi ganawar sirri tare da gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.

An fara ganawar ne da misalin karfe 11:30 na safe a ofishin shugaban kasa.

Ganawar ya kasance daya daga cikin na karshe da shugaban kasar zai yi a villa kafin ya lula zuwa kasar Saudiyya sannan daga bisani zuwa birnin Landan.

Har yanzu Gwamnan na CBN na ofishin shugaban kasa a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

KU KARANTA KUMA: Ana saura kwana 5 auranta ruwa ya yi awon gaba da ita (hotuna)

A baya Legit.g ta rahoto cewa bayan halartan taron karfafa tattalin arziki a Saudiyya, shugaba Muhamadu Buhari zai garzaya kasar Ingila da sunan ziyarar kansa, imma hutawa ko jinya, kamar yadda yayi a baya.

Buhari ba zai dawo Najeriya ba sai ya kwashe makonni biyu a birnin Landan, zai dawo ranar 17 ga Nuwamba, 2019.

Mun kawo muku rahoton cewa a ranar Litinin ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, zai bar Abuja zuwa birnin Riyadh na kasar Saudiyya domin halartar wani taro na masu saka hannu jari (FII) da hukumar samar da kudaden kasuwanci ta kasar Saudiyyya (PIF) ta shirya.

Za a fara taron ne daga ranar 29 ga wata zuwa ranar 31 ga watan Oktoba, kuma za a tattauna ne a kan harkokin bunkasa kasuwanci ta hanyar fasahar zamani.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel