Yadda na shiga masana'antar Kannywood, in ji Sunusi Oscar 442

Yadda na shiga masana'antar Kannywood, in ji Sunusi Oscar 442

Sunusi Hafeez wanda aka fi sanida Sunusi Oscar 442 sanannen mai bada umarni ne a masana'antar Kannywood. Mai bada umarnin ya bayyana yadda ya shiga masana'antar Kannywood.

Ya bayyana cewa, ya girma a garin Kano ne a karamar hukumar Fagge ta jihar. Ya kasanace mai son kallon dirama bayan ya tashi daga makaranta. daga nan ne ya fara son lamarin tare da shigewa masu shiryawa. A hakan ne kuma ya fara bayyana musu kurensu.

Daga baya ya bawa wasu abokansa shawarar fara sana'ar fim amma kuma babu jari. Daga baya kuma ya samu kudin fara shirya fina-finansa na kansa.

KU KARANTA: Safiyya Ahmad, ta lashe gasar Hikayata na bana

Da aka tambayi daraktan yadda ya zama darakta bayan a furodusa kuma dan wasa ya fara a masana'antar, sai yace, "Tun farko ni inasson gyaran kure ko a lokacin. Duk abinda bai min ba nakan gyarashi. Toh daga nan ne na fara gwada sa'ata a fannin bada umarni. Shekaru 20kenan da suka shude. Tun daga nan kuwa na cigaba da bada umarni,"

Oscar ya bayyaan burinsa na zama mai bada umarni a masana'antar Bollywood har da Nollywood. ya kuma tabbatar da cewa, ba zai sassauta ba wajen cika wannan burin nasa. baya fatan ya kammala aikinsa da masana'antar kannywood kadai

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel