Jami’ar Jihar Taraba ta sallami sabon ‘Dalibin da ke sukar Gwamna Darius Ishaku

Jami’ar Jihar Taraba ta sallami sabon ‘Dalibin da ke sukar Gwamna Darius Ishaku

Jami’ar jihar Taraba da ke Garin Jalingo ta dauki tsattsauran mataki na sallamar ‘Dalibinta saboda yawan sukar gwamnan jihar, Mai girma Darius Ishaku da ya ke yi a shafinsa na Facebook.

Ana zargin cewa an kori Mista Joseph Israel wanda ya ke aji daya ne a jami’ar ta Jalingo saboda yadda yake fitowa shafinsa na sada zumunta na Facebook ya na sukar Mai girma gwamnan jihar.

Hukumar jami’ar ta labe da cewa dalilin korar Joseph Israel shi ne rashin cike fam din aka ba sa na rantsuwa, sannan kuma bai halarci bikin da ake shiryawa sabon shiga jami’ar da aka yi ba.

Kamar yadda jaridar Premium Times ta rahoto jiya Laraba, 9 ga Watan Oktoba 2019, jami’ar ta bayyana wannan ne a wata takarda da fito daga ofishin mataimakin Magatakardar jami’ar jihar.

KU KARANTA: Mataimakin gwamna ya damke masu sabawa dokar titi a Legas

Jami’in mai suna Yakubu Fwa wanda ke lura da sha’anin karatun ‘daliban jami’ar ne ya sa hannu a wannan takarda inda yace daga yanzu an sallami Joseph Isreal domin ba a san da zamansa ba.

Wani fitaccen ‘dan gwagwarmaya, Jen Jibrin, ya sanar da Jaridar cewa ainihin laifin ‘Dalibin da ake gani shi ne sukar gwamnan da yake yi. A cewarsa an labe ne da wancan laifi don a koresa.

Jibrin yace shafin Israel kaca-kaca yake da suka a kan gwamnatin Ishaku. Kwanaki ‘dalibin ya fito yana cewa motoci 7 kurum gwamnan zai saida a Tawagarsa domin jami’ar jihar ta mike.

Kin halartar bikin rantsuwar shiga jami’a bai zama laifin da ake yi wa hukunci da kora. Sai dai kwanakin baya an taso ‘Dalibin mai karantar ilmin sinadarai a gaba da zargin satar jarrabawa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel