Shehu Sani: Bai dace a rika kama Mawakan da su tare da Gwamnati ba

Shehu Sani: Bai dace a rika kama Mawakan da su tare da Gwamnati ba

Kwamred Shehu Sani ya fito ya yi tir da kamen da ake ta yi wa wasu daga cikin Makada da Mawakan Hausa. Sanatan ya nuna takaicinsa da damke wasu Mawakan na Arewa da aka tsiro.

Kawo yanzu dai an kama wasu manyan Mawakan da ake ji da su a Arewa irin su Aminu Ladan Abubakar wanda aka fi sani da Alan Waka da kuma Naziru Sarkin wakan Sarkin Birnin Kano.

Sanata Shehu Sani a shafinsa na Tuwita yake cewa kame da tsangwamar da ake yi wa wadannan Mawaka da ke amfani da basirar su wajen sukar gwamnati da masu mulki, sam dai dace ba.

A daidai wannan lokaci kuma tsohon ‘Dan majalisar dattawan na Najeriya yace ana jinjinawa sauran Makada da Mawakan gwamnati da ke yawan caccakar masu adawa da gwamnati mai-ci.

Jama’a na yawan kukan cewa a maimakon ace ana kama Mawakan APC ana kai su kotu da sunan batanci, sai ya zama an maida su ‘yan kazanagin gwamnati wadanda ake yabawa basirarsu.

KU KARANTA: Shehu Sani ya yi wa Jonathan da Buhari kudin goro ya soke su

Tsohon Sanatan na Kaduna yace wannan abu da yake faruwa a Arewacin kasar bai dace ba. Sani ya yi wannan jawabi ne a shafin sa na Tuwita a Ranar Litinin, 16 ga Watan Satumba, 2019 da safe.

Kwamred Sani yake cewa: “An kama hanyar tsangamawa Mawaka da Makadan Arewa, wadanda ke amfani da wake-wakensu cikin harshen Hausa wajen sukar mummunan mulkin gwamnati…”

Jawabin na sa ya kara da: “…tare da kuma tasa keyar masu rike da madafan iko a gaba; yayin da su kuma Mawakan da ke yabon gwamnati su ke sukar ‘yan adawa ke samun yabo da karbuwa.’

A karshe Sanatan wanda ya yi kaurin suna wajen kare hakkin Bil Adama tun a zamanin mulkin Soja yake cewa dole a yi Allah-wadai da wannan. Shafin na sa na Tuwita shi ne @ShehuSani

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel